'Yan bindiga sun yi awon gaba da sama da mutum 40 a Zamfara

'Yan bindiga

Asalin hoton, AFP

Wasu 'yan bindiga sun kai hari tare da sace mutane fiye da arba'in a garin Gobirawan Cali, da wasu mutum hudu a Magami na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a Najeriya.

'Yan bindigar sun kai harin ne a ranar Asabar da misalin karfe uku da rabi da rana.

Wani da ya tsallake rijiya da baya a yayin harin ya shaida wa BBC cewa, 'yan bindigar sun fara kokarin sace wani mutum ne inda suka yi kokawa da shi daga bisani mutumin ya samu nasara a kan dan bindigar da yake shi ma yana tare da makami a jikinsa.

''Nan da nan sai dan bindigar ya kwace makamin mutumin ya cilla cikin wata gona ya kuma gudu inji mutumin'' in ji wata majiya da ta yiwa BBC karin bayani.

Jim kadan ba a jima ba sai ayarin 'yan bindigar suka shiga garin suka bude wuta suna kuma kora jama'a.

Ganau din ya ce,"Akalla an sace mutum sama da arba'in a yayin wannan hari amma kuma wasu daga cikinsu sun samu sun kubuta".

Ya ce,"Bamu samu mun sanar da jami'an tsaro wannan hari ba saboda duk layukan sadarwar da ake da su basa aiki a garinmu".

Ya kara da cewa "A yanzu garinmu na Gobirawan Cali duk ba kowa an gudu saboda wannan bala'i, don haka mu a yanzu bamu da ranar komawa garinmu har sai gwamnati ta samar mana da jami;an tsaro".