Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ings, Bale, Costa, Eriksen, Telles, Sorloth

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham na son dauko dan wasan Southampton da Ingila Danny Ings, mai shekara 28. (Football.London)
Manchester United za ta biya kusan euro 20m euros (£18.5m) idan tana son dauko dan wasan Real Madrid da Wales Gareth Bale, mai shekara 31. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Juventus ta sanya Douglas Costa a kasuwa. A baya an yi hasashen cewa Manchester United za ta dauki dan wasan na Brazil mai shekara 29. (Goal)
Za a iya barin dan wasan tsakiyar Denmark Christian Eriksen, mai shekara 28, ya bar Inter Milan watanni kadan kawai bayan zuwa kungiyar daga Tottenham. (Calciomercato - in Italian)
Arsenal na son dauko golan Iceland Runar Alex Runarsson, mai shekara 25, kuma ta soma tattaunawa da Dijon a kan batun. (Telegraph)
Porto ta rage farashin da ta sanya kan dan wasan Brazil Alex Telles zuwa euro 20m (£18.5m), kuma rahotanni na cewa Manchester United na zawarcin dan wasan mai shekara 27. (A Bola - in Portuguese)
Tottenham na iya fafatawa da Manchester United a yunkurin dauko dan wasan Real Madrid da Sufaniya Sergio Reguilon, mai shekara 23. (Mail)
Kazalika Tottenham na tattaunawa da Trabzonspor kan yarjejeniyar dauko dan wasan Norway Alexander Sorloth. Kungiyar ta karbo aron dan wasan mai shekara 24 na shekara biyu daga Crystal Palace kuma wajibi ne kungiyar ta kasar Turkiyya ta saye shi idan ya murza musu leda ta rabin kakar wasan bana. (Express)
Newcastle ta nemi karbo aron dan wasan Roma da Turkiyya Cengiz Under. Leicester ma tana son dauko dan wasan mai shekara 23. (Inside Futbol)
Bournemouth ta bukaci Leicester ta biya £50m idan tana son dan wasan tsakiyar Wales David Brooks, mai shekara 23. (Sun)











