Gwamna Tambuwal ya shaida wa BBC inda ake kai kudaden da ake cirewa daga albashin ma'aikatan Sokoto

Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da ake da karancin yara mata masu zuwa makaranta
    • Marubuci, Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-media Broadcast Journalist

Ga alama matsalar ilimi, musamman batun samar da gidauniya ta musamman domin farfado da ilimi a jihar Sokoto ne ta fi jan hankali a tattaunawar da BBC ta shirya tsakanin gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu daga cikin al'ummar jihar.

Baya ga wadanda suka yi tsokaci a lokacin tattaunawar, BBC ta samu korafe-korafe game da cewar ana cire wa ma'aikatan jihar wani kaso daga cikin albashinsu a matsayin gudumawarsu wajen farfado da ilimin jihar.

A cewar wasu daga cikin masu koken har yanzu ba za su iya nuna abu guda daya da aka aiwatar da kudaden da aka tara ba.

Arewacin Najeriya na da yara marasa zuwa makaranta mafi yawa a kasar

Umar Abdullahi ya ce: "Sanin kowa ne an kafa wani kwamiti, wanda mai girma gwamna ya kafa da kansa, ana debe wa ma'aikatn Sokoto kudi daga cikin albashinsu a kan cewa za a ciyar da ilimi gaba. Yau tsawon shekara hudu da watanni, wannan kwamiti ba wani aiki da ya yi a jihar Sokoto, babu wata makaranta a jihar Sokoto da take da isassun kujeru ko kayan aiki, ba a kula da dalibai…An ce kudaden suna hannun wani, amma gwamna shi ke da hakkin yi wa al'ummar jihar Sokoto bayani kan inda dukiyarsu take".

Sai dai a lokacin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya amsa tambayar ya ce ma'aikatan jihar Sokoto ne suka amince da kansu wajen ganin an gudanar da wannan tsari, inda ake cire wani kaso daga kowane ma'aikaci tun daga kan gwamna har kasa.

Nawa aka tara?

A lokacin da aka tambayi gwamnan game da ko nawa aka tara a cikin asusun tun bayan da aka kafa shi sama da shekara 3 da suka gabata, sai ya ce "A nawa sani, magana ta karshe da muka (kudaden da aka tara) sun kai kusan Naira biliyan daya."

Ina kudaden suke?

A cewar gwamnan: "Tun da aka kafa wannan kwamiti muka yi shawarar cewa ubanmu a jihar Sokoto shi ne mai alfarma sarkin musulmi, shi muka ba jagorancin wannan kwamiti tare da sauran wasu dattijai a cikin jihar. Shekara-shekara wannan kwamiti kan bayyanar da abin da aka yi kuma ya bayyana abin da ke cikin asusun."

Batun da mutane suka fi yin tambayoyi a kai su ne Ilimi da kayan more rayuwa

Gwamnan ya kuma ce ba gazawa ce ta sanya aka ki barin aikin kulawa da asusun farfado da ilimi na jihar a hannun gwamnatin jiha ba, hasali ma akwai wakilcin ma'aikatan gwamnatin a cikin kwamitin.

Me aka yi da kudaden?

Gwamnan ya ce ya zuwa ranar da aka yi wannan tattaunawa yana da tabbacin cewa an kammala ginin sabbin makarantu kusan 12 daga cikin wannan asusu. Sai dai ya ce ba ya da tabbacin ko makarantu nawa ne aka gyara daga cikin wadannan kudade.

Game kuwa da maganar kujerun karatu Aminu Waziri Tambuwal ya ce gwamnatinsa ta samar da kujeru sama da 150,000 wadanda aka raba a makarantun jihar.

Ilimin yara mata

Wata mai suna Naja'atu Dahiru ita ma ta yi tambaya a kan ko gwamnatin ta jihar Sokoto ta dauki wasu matakai na bunkasa ilimin yara mata.

An yi tambayoyi kan lafiya daci gaban matasa

Inda gwamnan ya ce ya kirkiro hukumar kula da ilimin yara mata domin bunkasa yadda za a habbaka bangaren. Ya kuma ce gwamnatinsa a yanzu haka ta fara aikin gina kananan makarantun sakandare na mata guda daya a kowace karamar hukumar jihar.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa tare da hadin gwamnatin tarayya sun kashe kudi akalla Naira biliyan 15. "Gwamnatin jiha ita kanta ta kashe akalla kusan Naira biliyan 10 a matsayin nata kaso domin ganin an gyara makarantu an kuma kawo kayan aiki".

'A yi wa masu fyade daurin rai-da-rai'

Wata mai suna Halima Abubakar ta tambayi gwamnan game da matakin da jihar za ta dauka wajen tunkarar matsalar fyade da ake fama da ita a jihar. A lokacin da gwamnan ya amsa wannan tambaya ya ce yanzu haka akwai dokar hukunta masu fyade a jihar wadda ta tanadi dauri ga duk wanda aka kama da laifi. Sai dai a nasa bangaren ya ce zai so a rinka yi wa masu fyade daurin rai-da-rai a matsayin hukunci kan abinda suka aikata.

Haka nan ma Farida Abubakar ta yi tambaya kan shirin inshorar lafiya ga al'ummar jihar. Inda gwamnan ya ce shirin ya samu cikas daga farko bayan da wasu mutane daga jihar suka yi tunanin cewa shiga shirin inshorar ya ci karo da tanadin addinin musulunci. Sai dai a cewar sa yanzu haka gwamnati ta fara aiwatar da shirin inda ta zuba makudan kudade wadanda za su isa a fara kulawa da akalla mutum dubu biyu zuwa dubu biyar.

Wasu mutanen Sokoto sun aiko da tambayoyinsu ta sakonnin bidiyo

Mabera

Baya ga ilimi abu na biyu da mutane suka fi kokawa a kai shi ne matsalar rashin hanyoyi da magudanun ruwa a unguwar Mabera da ke cikin garin Sokoto.

Wani da ya yi tambaya kai-tsaye ta manhajar 'Zoom' Mansur Mabera ya yi ikirarin cewa tun a wa'adin mulkin gwamnan na farko ne ya yi wa al'ummar yankin alkawarin hanyoyi da magudanan ruwa sai dai har yanzu ba a cika alkawarin ba. Haka nan ma Umar Abdullahi ya fadi cewa mutane ba su son zuwa unguwar saboda matsalar hanya.

Gwamnan ya bayyana cewa ya je unguwar da kansa kuma ya sa an yi taswirar aikin da za a yi, inda gwamnatin jihar ta hada hannu da bankin duniya kan wani shir da ake kira 'New Map' domin samar da hanyoyi da magudanan ruwa a shiyyar, har ma da aikin madatsar-ruwa ta noman rani a Wurno.

BBC na hada tattaunawa ne domin tunatar da 'yan siyasa kan alkawurran da suka dauka

Gwamnan ya ce tun shekara uku da suka gabata gwamnatinsa ta biya Naira biliyan daya da rabi a matsayin nata kason na ayyuakan magudanan ruwa da hanyoyi a Mabera da wasu ayyuka a sassa daban-daban na jihar.

'Ina mamakin har yanzu ana matsalar ruwa a Sokoto'

A lokacin da aka tambaye shi game da koken da mutanen yankin Minannata da kuma wasu yankuna na birnin Sokoto suka yi kan rashin ruwan fanfo, gwamnan ya ce yana mamakin yadda ake cewa ana samun matsalar ruwa a birnin na Sokoto.

Ya ce "Gwamnati tana kashe kusan Naira miliyan dari da arba'in a kowane wata domin ganin kwaryar birnin Sokoto ta samu ruwa".

Za ku iya kallon cikakken shirin na bidiyo a BBC Hausa YouTube

A FADA A CIKA shiri ne da BBC Hausa ke shiryawa tare da tallafin gidauniyar MacArthur