World Trade Organization: Yadda ɗan Afirka zai kawo sauyi a shugabancin Kungiyar Cinikayya Ta Duniya

Yayin da uku daga cikin 'yan takarar shugabancin Ƙungiyar Cinikayya Ta Duniya wato World Trade Organization (WTO) suka fito daga Afirka, editan sashen kasuwanci na BBC Africa Zawadi Mudibo ya duba tasirin da za su iya yi kan nahiyar idan suka samu shugabancin.

'Yan difilomasiyyar Afirka na da babban burin cewa ya kamata a ce ɗan Afirka ya zama shugaban ƙungiyar WTO, babbar cibiyar kasuwanci ta duniya.

A lokacin da Ba'amurke ne ya yi ta shugabancin Bankin Duniya sannan kuma Bature ne ya yi ta shugabancin Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, ɗan Afirka bai taɓa shugabanci a makamancin waɗannan cibiyoyi ba.

Amma idan ɗaya daga cikin Ngozi Okonjo-Iweala ta Najeriya ko Amina Mohamed ta Kenya ko Abdel-Hamid Mamdouh na Masar ya zama shugaba, Nahiyar Afirka za ta ji cewa lallai tana da rawar takawa a harkar kasuwancin duniya.

WTO na tabbatar da dokokin kasuwanci a duniya sannan ta shiga tsakanin ƙasashe yayin da aka samu saɓani. Sannan ta "kafa harkokin kasuwanci ga kowa da kowa," kamar yadda shafinta ya bayyana.

Ƙungiyar da ke da mazauni a birnin Geneva, na da tasirin da take iya jan hankalin kowacce ƙasa ta saka hannu kan dokokin kasuwanci. Haka ma shugabanta yana da ƙarfin faɗa a ji.

Shugaban mai laƙabin darakta-janar, yakan halarci taron G7 na ƙasashe bakwai mafi ƙarfin tattalinh arziki da kuma na G20 sannan kuma yana iya sasanta tsakanin shugabannin ƙasashen duniya.

Sai dai, ko akwai wani abu da Afirka za ta amfana da shi baya ga difilomasiyya?

'Kasuwanci ba tallafi ba'

Duk da cewa ofishin shugaban ƙungiyar ya fi ga shugabanci kawai, amma yana da ikon tabbatar da cewa ana ɗaukar muradun Afirka a cikin harkokin WTO.

Ba kowa da kowa ne ake sa ran su fahimci yadda ake yin tattaunawar kasuwanci ba, amma sakamakonsu kan shafi rayuwar kowa da kowa.

Tun daga kan ɗan kasuwar da ke zirga-zirga ba adadi koanne wata, zuwa ga kwastoman da ke sayen kayan da aka shigo da su cikin ƙasa, zuwa ma'aikatan kamfani: dukkanin dokokin kasuwanci sun shafe su.

Ana kallon kasuwanci a Afirka a matsayin hanyar haɓaka, hanya zuwa ga cigaba da kuma kayan aikin yaƙar talauci.

"Tallafi daga ƙasashen waje ba zai taɓa yi ba a Afirka. Kamar yadda aka sani a tarihi a ko'ina, kasuwanci ne," a cewar David Luke shugaban cibiyar Economic Commission for Africa ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

"Saboda haka 'yan Afirka za su fahimci cewa idan ɗan Afirka na shugabancin WTO hakan na nufin da gaske muke yi game da kasuwanci."

Shimfiɗaɗɗiyar hanyar kasuwanci a Afirka

Misis Okonjo-Iweala, tsohuwar ministar ƙudi a Najeriya, ta faɗa wa BBC cewa talakan Afirka kawai ta fi damuwa da shi.

Ta ce za ta lalubo hanyyoyin "yadda mata da matasa waɗanda su ne ke tafiyar da harkokin cigaban Afirka za su amfana da ƙungiyar kasuwancin ta duniya".

Sannan tana so ta tabbata cewa Afirka ta daina shigo da kayan sarrafawa na masana'antu, maimakon haka "a ƙara kyautata abin da muke sarrafawa domin amfanin kasuwannin duniya.

"Misali, muna sayo kashi 94 na kayayyakin haɗa magunguna alhalin za mu iya samar da su a nan cikin gida."

Misis Mohamed wadda ta riƙe muƙaman ministar kasuwanci da harkokin waje a Kenya, ta shaida wa BBC cewa za ta bijiro da "sabuwar hanya faffaɗa kuma dunƙulalliya a aikin".

Sai dai ta ce ba ta so a riƙa yi mata kallon "shugaba daga Afirka ko kuma mace, sai dai ƙwararriyar shugaba mai haɗa kan al'umma".

A nasa ɓangaren, Mista Mamdouh wanda ya riƙa wakiltar ƙasar Masar a ƙungiyar ta WTO tun shekarar 1985, ya ce ƙwarewarsa za ta a cikin ƙungiyar za ta bai wa Afirka damar amfana.

"Abin da na saka a gaba shi ne cusa 'yan Afirka cikin harkokin kasuwanci," in ji shi.

"Sannan zan yi kira ga 'yan kasuwar Afirka su mayar da hankali musamman kan tsare-tsaren kasuwanci."

Sai dai abin lura a nan shi ne, duk da cewa shugaban ƙungiyar ka iya shawo kan shugabanni, ba zai iya tilasta musu aikata wani abu ba.

Jerin sunayen 'yan takarar shugabancin WTO:

  • Mohammad Maziad Al-Tuwaijri - Saudiyya
  • Liam Fox - Birtaniya
  • Jesús Seade Kuri - Mexico
  • Abdel-Hamid Mamdouh - Masar
  • Amina Mohamed - Kenya
  • Yoo Myung-hee - Koriya ta Kudu
  • Ngozi Okonjo-Iweala - Najeriya
  • Tudor Ulianovschi - Moldova

Bugu da ƙari, idan ana neman taimaka wa Afirka wurin kafuwar tsarin kasuwanci na African Continental Free Trade Agreement (AfCFTA), shugaban WTO zai taimaka.

Yarjejeniyar da aka dakatar da aiwatarwa saboda annobar korona, tana fatan kafa wata hanyar kasuwanci maras shinge mafi girma a duniya.

"Hakan zai bayar damar samar da kayayyaki daga nahiyar, abin da kuma zai ƙara yawan kuɗi a aljihun mutane wanda kuma zai taimaka wurin rage talauci," in ji masanin kasuwanci Luke.

Ƙa'idoji da sharuɗan yarjejeniyar AfCTA sun yi daidai da na WTO kuma shugaban ƙungiyar daga Afirka zai iya taimakawa wurin kafuwa da kuma haɓakarta.