Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da suka kamata ku sani game da sabon tsarin kuɗin wutar lantarki a Najeriya
A farkon watan nan na Satumba ne kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya suka fara amfani da sabon farashin wutar lantarki a kasar.
Sun dauki matakin ne bayan sauyin da hukumar sanya ido kan harkokin wutar lantarki ta kasar wato NERC ta yi.
Sabon tsarin ya karkasa masu amfani da wutar zuwa gida biyar inda karfin aljihun kowane ma'aunin wutar da za a ba shi.
Mai magana da yawun kamfanin raba wutar lantarki da ke kula da jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa, Ibrahim Sani Shawai, ya shaida wa BBC, cewa an karkasa tsarin ga bangarori daban-daban.
Rabe-raben yadda matakan suke
- Masana'antu
- Kamfanoni
- Ma'aikatun gwamnati
- Unguwannin masu hannu da shuni.
- Unguwannin talakawa
"Irin wadannan aka wawware hanyoyin da suke kai musu hasken wutar lantarki. Amma duk da haka idan kuka hadu a unguwarku kuna so a saka ku a Mataki na A, amma mu kuma a tsari mun sanya ku a Mataki na C, za ku iya zuwa ku tattuana da hukumar rarraba hasken wutar lantarki ku ce kuna so a kai ku Mataki na A saboda za ku iya biyan kudin hasken wutar lantarki matakin," in ji Shawai.
A cewarsa: "Wannan sabon tsari ne da zai bai wa al'umma dama na yin zabi yadda za su samu hasken wutar lantarki. Hakan na nufin cewa daga yanzu iya kudinka iya shagalinka."
Iya kudinka iya shagalinka
- Mataki na A - Wadanda ke wannan mataki za su samu wutar lantarki ta tsawon awa 20 zuwa sama.
- Mataki na B - Na bayar da damar samun wutar lantarki ta tsawon awa 16 zuwa 20
- Mataki na C - A wannan mataki za a samu wutar lantarki ta tsawon awa 8 zuwa 12
- Mataki na D - Awa 4 zuwa awa 8
- Mataki na E - Awa 4 zuwa awa 8
Matsalar wutar lantarki a Najeriya
Rashin wutar lantarki a Najeriya a iya cewa na daga cikin manyan abubuwan da suka karya lagwan tattalin arzikinta, musamman ma ta bangaren masana'antu.
Kamfanoni da dama sun rufe harkokinsu a kasar sun koma wasu kasashen Afirka saboda rashin wutar lantarki a Najeriya kamar yadda rahotanni suka sha bayyanawa.
Gwamnati ta sha bullo da matakai da dama da zummar magance matsalar, sai dai har yanzu 'yan kasar na kokawa a kan wannan matsala.
An warewa bangaren makudan kudade karkashin yarjejeniyoyin da gwamnati ta cimma da kamfanonin kasashen waje daban-daban da zummar samar da hasken wutar lantarki, sai dai wasu na ganin cewa har yanzu bata sauya zani ba.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, na bugun kirjin cewa ta samar da karin kuzarin wutar idan aka kwatanta da yadda ta tarar da ita, amma wasu na cewa ci gaba ne irin na mai hakar rijiya.