Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙungiyar ISWAP ta ce ita ta kashe sojojin Najeriya a Kukawa
Ƙungiyar IS ta ce ta kashe sojojin Najeriya guda bakwai a garin Kukawa da ke jihar Borno a arewacin Najeriya, yayin da rahotanni suka ce kuma mayakan sun kuma yi garkuwa da mutane da dama a garin.
A sanarwar da ta fitar IS ta ce mayakanta sun kai hari sansanin Soji inda suka yi artabu da su, tare da ikirarin kashe mutum bakwai da raunata wasu.
Sannan ƙungiyar ta ce ta kwace motocin yaki da makamai na sojojin Najeriya.
Sai dai ba ta bayyana cewa ta yi awon gaba da mutanen garin na Kukawa ba a harin da ta kai ranar Talata.
A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da harin amma ta yi ikirarin murƙushe mayakan. Ko da yake sanarwar ta ce akwai sojoji uku da suka samu mummunan rauni.
Sanarwar da kakakin rundunar sojin Najeriya Janar John Enenche ya fitar ta ce sojoji sun kashe ƴan Boko Haram takwas yayin da wasu kuma da dama suka tsere da rauni a jikinsu.
Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari garin Kukawa tare da hana mutane fita daga cikinsa.
Harin, na zuwa kwanaki kaɗan bayan da ɗaruruwan ƴan gudun hijira suka koma garin da zama.
Labarin harin ƙungiyar ya nuna yadda har yanzu suke da sauran karsashi duk da ƙoƙarin da sojojin ƙasar ke yi na murƙushe su.
A makon da ya gabata ne ɗaruruwan ƴan gudun hijira da aka raba da muhallansu suka koma garin da zama - an shaida musu cewa a yanzu garin na cikin aminci.
Kusan mutum miliyan biyu rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa har yanzu akwai sauran matsala saboda taimakon hukumomin jin ƙai ba ya iya kai wa ga rabin mutanen.