Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Riga-kafin Coronavirus: Putin ya ce za a fara amfani da riga-kafin cutar
Shugaban Russia Vladmir Putin ya sanar da cewa ƙasar ta fitar da rigakafi na farko a duniya na annobar cutar korona.
Duk da rashin amincewar masana kiwon lafiya da kuma gargaɗi daga Hukumar Lafiya ta Duniya a bi a hankali, ministan lafiya Mikhail Murashko ya bayyana cewa maganin an "tabbatar yana da tasiri da aminci".
Ministan ya ƙara da cewa za a ci gaba da gwada maganin a kan daruruwan mutane.
Putin ya ce 'yarsa daya ta yi amfani da maganin kuma ta warke daga ƙaruwar zazzaɓin da ta yi fama da shi.
Akwai riga-kafi da yawa da ake tsaka da samarwa a ƙasashe da dama. A farkon watan nan ne ƙwararren likitan Amurka Dakta Anthony Fauci ya ce yana fatan "da gaske Rasha tana gwada maganin" kafin fara amfani da shi.
Jami'ai sun ce suna shirye-shiryen fara bayar da riga-kafin ga mutane da dama a watan Oktoba.
Ƙwararru sun nuna damu kan saurin aikin samar da riga-kafin da Rasha ta yi, suna cewa mai yiwuwa masu bincike sun yi coge ne.
A yayin da ake tsaka da fargaba kan zama cikin aminci, Hukumar Lafiya Ta Duniya ta nemi Rasha a makon da ya gabata da cewa ta bi matakan kasa da ƙasa na samar da riga-kafin cutar korona.
A ranar Talata, WHO ta ce tana tattauna wa da hukumomin Rasha a kan sake duba salon samar da riga-kafin.
A yanzu haka, riga-kafin na Rasha baya daga cikin jerin wadanda WHO ta amince da su da suka kai matakai uku na gwaji, da ya haɗa da gwaje-gwaje sosai a kan ɗan adam.
Me Shugaba Putin ya ce kan riga-kafin?
Da yake bayyana shi a matsayin na farko a duniya, Shugaba Putin ya ce riga-kafin, wanda cibiyar lafiya ta Gamaleya da ke Moscow ta samar, zai kasance "garkuwa" game da cutar korona
Ya kara da cewa yana sane cewa riga-kafin "zai yi aiki sosai", ba tare da yin cikakken bayani kan abin da yake nufi ba, amma ya ce ya tsallake dukkan gwaje-gwajen da "ake bukatar yi a kansa".
Kazalika a karin bayanin da ya yi game da yadda 'yarsa ta yi amfani da riga-kafin, Mr Putin ya ce: "Bayan an yi mata allurar farko, yanayin zafin jikinta ya kai digiri 38, washegari ya yi kasa zuwa digiri 37.5, kuma shikenan. Bayan an yi mata allura karo na biyu, yanayin zafin jikinta ya yi sama kadan, sannan ya sake zama daidai."
Ba kasafai Shugaba Putin yake magana kan 'ya'yansa mata - Maria Vorontsova da Katerina Tikhonova a bainar jama'a ba - kuma kusan dukkan rayuwarsu a cikin sirri take.