Yadda ake rasa rayuwa wajen neman dutse mai daraja a Myanmar

- Marubuci, Daga Soe Soe Htoon da Rebecca Henschke
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Si Thu Phyo na tattara dan abin da ya rage na dutsen a lokacin da ya ji karar girgiza a kusa da shi.
Mutumin mai shekara 21 mai kwazo ne a daya daga cikin inda ake hakar wani dutse mai daraja a jihar Kachin da ke arewacin Myanmar.
Yana daga cikin daruruwan mutanen da suke kwasar dutsen tsautsayi ya rutsa da su.
Ya yi kokarin guduwa, amma sai kasa ta rufta da shi kan kace kwabo baraguzan duwatsu sun danne shi.
Si Thu, ya fada ruwa, ya ce " duk bakina ya cika da turbaya, duwatsu duk sun buge ni yayin da igiyar ruwa kuma ta kwashe ni ta kai ni wani waje can daban, ni na zaci mutuwa ma zanyi".
To amma Si Thu ya samu ya kubuta inda aka kai shi asibiti ya fuskanci cewa bakwai daga cikin abokansa da suka je wajen duk sun mutu, suna ma cikin mutum 200 da suka mutu a wannan wajen hakar duwatsun.
Ya ce " Muna zaune ne tamkar 'yan uwa, tare muke bacci a gado guda".
Daga gidan da yake zaune shi da iyalansa yana iya hango tsaunin da ake hako dutsen mai daraja.
Ya ce ' Bana jin dadi saboda ina daga cikin wadanda suka rayu a wannan rana, dama a ce mafarki nake na tashi naga abokaina a kusa dani".


Ana samun mummunar zaftarewar kasa a kusan kowacce shekara a lokacin damuna a wajen hakar ma'adinai da ke jihar Kachin.
Akan samu kaso 70 cikin 100 na dutse mai daraja a wannan mahaka abin da ya sa ake samun makudan kudade wajen cinikinsa..

Saboda matsin lamba daga bangaren jama'a ya sa gwamnatin Myanmar ta nada wani kwamiti karkashin jagorancin ministan kula da albarkatun kasa da muhalli domin yin bincike a kan zaftarewar kasar da ta haddasa mutuwar daruruwar mutane a wajen hakar dutse mai daraja.
An kafa kwamitin ne da nufin bincike da kuma tsara yadda za a biya iyalan wadanda suka mutu a wannan iftila'i diyya.
Yanzu haka kwamitin ya kammala bincikensa har ma ya zauna da shugaban kasar amma kuma ba a sanar wa jama'a sakamakon binciken ba
To sai dai ministan albarkatun kasar Ohn Win, ya ce yawancin masu hakar wannan dutse zalama ce ke kai su.
Ministan ya ce daga yanzu a hukumance za a daina hakar dutsen a lokacin damuna.
Ita kuwa jagorar gwamnatin Myanmar, Aung San Suu Kyi ta ce rashin aikin da ya yi katutu a kasar ne ke janyo wannan matsala.

Yan Naing, dan shekara 23, an masa dinkin raunin da ya samu har 14.
Ya kammala karatun digirinsa, ammma saboda rashin aikin yi shi ma ya fara zuwa wajen hakar dutse mai daraja don ya samu dan kudin kashewa.

Wannan waje na hakar dutsen, waje ne da babu cikakkiyar doka a kan sa, saboda gwamnatin kasar bata da cikakken iko a kan wajen saboda yanayin mutanen yankin.
Masu sharhi dai na ganin cewa idan dai har ana so a kawo karshen asarar rayukan da ake yi a wannan waje, dole ne gwamnati ta sanya kwakkwarar doka da kuma sanya idanu a kan masu zuwa wannan waje.

Gwamnatin Myanmar dai na asarar miliyoyin daloli a wannan bangaren na hakar wannan dutse saboda yadda ake kwashe dutsen mai daraja ba bisa ka'ida ba.
Masana sun ce za a rinka amfani da kudaden shigar da za a rinka a samu a bangaren wannan dutse don Myanmar ta samu kudaden shiga masu yawa.

Si Thu, ya ce a lokuta da dama ya kan samu irin wannan dutse mai daraja da yawa, amma daga karshe sai wani kamfani ko kuma masu tayar kayar baya su kwace.
Ya ce " Akwai lokacin da wani abokina ya tara dutsen nan da yawa amma da ya fuskanci za a kwace masa sai ya watsa su a ruwa kawai bai ma tuna da wahalar daya sha ba kafin ya samu dutsen".


A wajen da kasa ta zaftare har ta yi sanadin mutuwar abokan Si Thu, an ajiye furanni a watan da ya shude saboda jimami a kan rashin da aka yi.
Wani babban malami ne ya jagoranci taron addu'oin da aka yi wa mamatan.
Daruruwan mutane ne suka samu damar halartar taron addu'ar.

Daga cikin wannan taro akwai Daw Mu Mu, wadda ta yi tafiyar sa'a 20 daga Mandalay domin neman danta mai shekara 37 wato Ko Yarzar.
Ta ce " A kodayaushe naji ance an gano wata gawa sai na je na duba, kafafuna duk sun kumbura saboda hawa da sauka kan wannan tsauni".
Tana son taga gawar danta domin ta samu dala 2,500 na diyya wanda gwamnati da kuma hukumomin agaji suka ce za su bayar.
Ta ce " Na san na rasa shi, amma ina fatan naga gawarsa, a yanzu a dakinsa nake kwana domin kewarsa, sannan na kan dauki kayansa da ya ke sawa a lokacin yana raye na rinka duba wa don su debe mini kewa".

Wata guda bayan an samu wannan iftila'i, mutane sun fara komawa wajen hakar dutsen, daga ciki kuwa har da yara wanda ke tafiya tare da iyayensu don neman dutse mai daraja.
Wata rana an yi ruwan sama, Si Thu ya je wannan mahaka, yana jiran raunukansa su warke saboda ya koma ya ci gaba da neman dutse, tsaye yake a wajen da da kasa ta rufta da abokansa bakwai, ya kalli niusan wajen da suke hawa ya ce " Kai nan gaba guduwa zan yi tun kafin wani mummunan abu ya same ni a wannan waje".
Hotuna daga Phyo Hein Kyaw











