Coronavirus a Indiya: An sallami Aishwarya daga asibiti, ba a sallami Amitabh da ɗansa ba

An sallami Aishwarya Rai Bachchan da 'yarta Aaradhya daga asibiti bayan an yi musu gwajin korona an tabbatar sun warke.

Jarumar fina-finan na Indiya, kuma wacce ta taba samun lambar yabo a sarauniyar kyau ta duniya, sun bar asibitin Nanavati ne tare da 'yarta a safiyar ranar Litinin.

Mijinta Abhishek Bachchan, ya wallafa sakon godiya a shafinsa na tuwita inda yake gode wa 'yan uwa da abokan arziki saboda addu'ar da aka yi musu shi da iyalansa da ma mahaifinsa a kan samun sauki daga cutar korona da suka kamu da ita.

Sai dai Abishekh da mahaifinsa Amitabh Bachchan har yanzu suna asibitin inda suke karbar magani.

A farkon watan da muke ciki ne aka kwantar da su a asibiti bayan an yi musu gwaji an ga suna dauke da cutar korona.

Aishwarya da 'yarta sun godewa jama'a saboda addu'oin da aka yi musu, kuma tuni suka koma gida.

Masoyan Amitabh da dansa a ciki da wajen Indiya na ci gaba da yi musu addu'a a kan samun sauki.

Amitabh mai shekara 77, fitaccen jarumi ne a Bollywood, kuma ya yi suna a duniya baki daya.

A ranar 12 ga watan Yuli ne ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa, ya kamu da cutar korona.

Jaya Bachchan, matar Amitabh wadda ita ma jaruma ce ba ta kamu da cutar ba bayan da gwaji ya nuna hakan.

Indiya dai ita ce kasa ta uku a yawan wadanda ke da cutar korona a duniya.

A ranar Litinin, an samu sabbin mutum 50,000 da suka kamu da cutar korona a cikin sa'a 24 a Indiya, abin da ya kai adadin wadanda suka kamu da cutar miliyan daya da dubu dari hudu.