Rikicin Benue: An kashe mutum bakwai a rikicin diyyar ma'adinai

Rundunar 'yan sandan jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya ta musanta rahotannin shafukan sada zumunta da ke cewa makiyaya ne suka kashe wasu mutane ranar Juma'a.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Logo inda aka zargi makiyaya da hada baki da wasu 'yan kabilar Jukun masu dauke da makamai wajen bude wa jama'ar kauyen Chembe da ke mazabar Ukemberegya/Tswarev a Logo wuta.

Sai dai sanarwar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Catherine Anene, ta fitar ranar Litinin ta ce lamarin ya faru ne sakamakon sabani tsakanin mutanen da suke raba kudin da aka samu daga sayar da wurin hakar ma'adinai.

"An gano cewa kamfanin da ke sarrafa ma'adinai ya biya kudin ga iyalan da ke kauyen Chembe kan wurin hako ma'adinai amma rikici ya barke kan wane ne hakikanin wanda ya mallaki wurin lamarin da ya kai ga hari abin da ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai", in ji Mrs Anene

Tun da fari dai Gwamna Samuel Ortom ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana makiyaya masu dauke da makami da ya zarga da kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba a matsayin 'yan ta'adda.

Gwamna Ortom dai ya dade yana neman a dauki mataki kan yadda a watannin baya-bayan nan 'yan bindiga ke kai hare-hare kan yankuna na jiharsa

Jaridar Guardian a kasar ta rawaito cewa da yammacin ranar 10 ga watan Yuli ne, wasu da ake zargi makiyaya ne suka yi hadaka da wasu 'yan kabilar Jukun masu dauke da makamai wajen bude wuta kan jama'ar kauyen na Chembe.

Jaridar ta ce akalla mutum bakwai ciki har da mace guda ne suka mutu yayin da wasu 12 har da yaro dan shekara 9 suke gadon asibiti.

Gwamnan jihar ta Benue ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a lamunce ba.

Ya ce: "Jihar Benue tana da doka da ta haramta yin kiwo a bainar jama'a. A don haka, kungiyar ta'addanci ce kadai za ta zabi karya dokar kamar yadda wadannan makiyayan suka yi tun bayan samar da dokar a 2017."

A cewarsa, bayyana makiyayan da ke dauke da bindiga a matsayin 'yan ta'adda zai kawo tabbatuwar doka da oda da kuma karshen rashin imanin da suke aikatawa.

Ya kuma nemi wadanda suke zaune a wuraren da rikicin ya shafa su rika sanar da hukumomin tsaro take-taken mutanen da basu yadda da su ba.

Sannan kuma ya yaba wa jami'an da ke aiki karkashin shirin Operation Whirl Stroke bisa azamar da suka yi wajen kai wa mutanen Tse-Chembe dauki.

Ya yi gargadin "babu wata barazana da hare-hare da za su hana aiwatar da dokar hana kiwo barkatai da samar da burtulai a jihar."

Rikici tsakanin manoma da Fulani makiyaya dai na ci gaba da zama wata gagarumar matsala, wadda ke barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasar.