Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
National Consultative Front: An kafa sabuwar ƙungiyar siyasa a Najeriya
Wasu fitattun masu fafutukar kare hakkin bil'adama da wasu kwararru sun kafa wata sabuwar kungiyar siyasa a Najeriya.
Cikin wata sanarwar da ta rarraba wa manema labarai, kungiyar ta ce ba ta fito ba sai da ta shirya, kasancewar 'ya'yan kungiyar sun shafe wata guda suna tuntubar juna, kana suka ga lokacin fitowa a sarari ya yi.
Sun dai kafa kungiyar mai suna National Consultative Front NCF, da nufin cusa sauyi a harkokin mulki da siyasa a Najeriya, sakamakon zargin da suke yi cewa jam'iyyun siyasar kasar na yanzu sun gaza da kuma nufin kaɗa guguwar sauyi a siyasa da harkokin mulki a Najeriya.
Mutanen da suka hada kungiyar sun hada da masu fafutukar kare hakkin bil'adama a fanni daban-daban, tare da hadin-gwiwa da gogaggun ma'aikata da manyan masana fiye da 30.
Wadanda suka kafa kungiyar sun yi zargin cewa jam'iyyun siyasar da suke mulki a matakai daban-daban a Najeriya sun gaza wajen kare rayukan al'umma daga matsalar tabarbarewar tsaro a kasar, musamman yadda ake fama da masifa ta kisa da satar jama'a a bangarori daban-daban na Najeriya da 'yan bindiga ke yi.
Dalilan kafa ƙungiyar
Kungiyar ta ce akwai rauni sosai tattare da wasu dokokin kasa, kasancewar su ba da kafar yi wa 'yan kasa kashin-dankali da kama-karya, har ta kai ga wasu da ta bayyana da "'yan ta-yi-dadi" kan samu damar hawa karagar mulki suna yin abin da suka ga dama…ta kai ga kuri'ar da jama`a ke kadawa a lokutan zabe ba ta da wani tasiri…tun da ba ta sakawa ko hanawa!
Kungiyar National Consultative Front ta ce ta fito ne ta yaki irin wannan matsala, ta hanyoyi da dama, ciki har da bazama lungu da sakon Najeriya don wayar da kan al'umma, tare da matsa-kaimi wajen ganin an aiwatar da wasu sauye-sauye ko garambawul ga kundin tsarin mulkin Najeriya.
Shan alwashi
Kungiyar ta yi alwashin tsayawa wajen ganin an yi gyara ko daidaita tafiyar Najeriya.
Daga cikin 'yan kugiyar akwai tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya, Ghali Umar Na'abba da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Obadia Mailafiya, da Sanata Shehu Sani da Obygeli Ezekwesili da Farfesa Jibrin Ibrahim.
Sau da dama kungiya irin wannan, da sannu kan rikide zuwa jam'iyyar siyasa.
Ko a gabannin babban zaben da aka yi a Najeriya, a bara, wasu sabbin jam'iyun sun yunkura, amma ba su ji dadin karo da manyan jam'iyyun siyasar kasar ba.