'Yan adawa da suka ka da shugabannin Afrika da ke kan mulki a zaɓe

A karshen makon jiya ne jagoran adawa na Malawi Lazarus Chakwera ya lashe zaben shugaban ƙasa zagaye na biyu inda ya kayar da Shugaba mai-ci Peter Mutharika.

Mr Chakwera ya lashe zaben ne da kashi 58.57 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaben da aka gudanar ranar Talata, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar ranar Asabar

Mun yi waiwaye kan wasu daga cikin 'yan adawa da suka doke shugabannin da ke kan mulki a zabukan kasashensu.

Yadda Buhari ya kayar da Jonathan a zaben 2015

A watan Maris na shekarar 2015 ne Muhammadu Buhari ya lashe babban zaben Najeriya, bayan samun nasara a kan babban abokin hamayyarsa Mista Goodluck Jonathan wanda ke kan karagar mulki a lokacin.

Gabanin wancan lokaci, ba a taba kayar da shugaban kasar da ke kan mulki a kasar ba.

Hukumar zaben kasar ta ayyana cewa jam'iyyar APC wacce Muhammadu Buhari, mai shekara 72 ya tsaya mata takara, ta samu kuri'a 15,424,921 yayin da Mista Jonathan na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a 12,.853,162

Nana Akofu-Addo ya kayar da John Mahama

A shekarar 2016, dan takarar jam'iyyar adawa ta NPP, Nana Akufo-Addo, ya kayar da Shugaba John Dramani Mahama a babban zaben kasar.

Mr Akufo-Addo ya lashe zaben ne da kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada inda abokin takararsa John Mahama ya samu kashi 44.

Wannan ne dai karon farko da shugaba mai ci ke shan kaye a zabe a tarihin kasar Ghana.

Kafin nasarar da ya yi a 2016, Akufo-Addo ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekarar 2012, inda suka gwabza da John Mahamma na Jam'iyyar NDC.

Zaben dai ya janyo ce-ce ku-ce, daga karshe kotun kolin kasar ta yanke hukuncin da ya raba kan alkalanta, kuma aka tabbatarwa da Mahama nasara.

Wasu masu sharhi a Ghana na ganin John Mahma ya sha kaye ne saboda tun da ya hau mulki ba shi da manufa ganin cewa ya gaji shugaban kasa John Attah Mills ne wanda ya mutu a kan mulki.

A shekarar 2017, Adama Barrow, wani fitaccen mai saye da sayar da gidaje, ya doke Shugaba Yahya Jammeh a zaben watan Disamba na shekarar.

Ya lashe zaben ne da kashi 43 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

A lokacin da yake yakin neman zabe, Mr Barrow ya sha sukar Shugaba Jammeh kan rashin sanya wa'adi biyu kawai ga duk wanda zai shugabanci kasar sannan ya soki daurin da aka yi wa 'yan jam'iyyun hamayya.

Jammeh ya hau mulkin Gambia a juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1994 inda ya kwashe shekara 22 yana mulki.