George Floyd: Trump ya bayar da umarnin ɗaure masu tumɓuke mutum-mutumi

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata dokar shugaban kasa wacce za ta sa a daure masu zanga-zanga idan suka tumbuke mutum-mutumin shahararrun mutane.
Dokar ta bukaci a "dauki tsattsauran matakin hukunci" kan duk wanda ya tumbuke ko ya lalata mutum-mutumin da aka kafa a wuraren da jama'a suke zuwa.
Dokar ta Mr Trump ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta rike kudaden kananan hukumomi da rundunonin 'yan sandan da suka gaza hana 'yan ta-more tumbuke mutum-mutumai.
An tumbuke mutum-mutuman fitattun mutane da dama a Amurka tun lokacin da aka soma zanga-zangar kyamar wariyar launin fata sakamakon kisan da 'yan sanda suka yi wa wani bakar fata da ba ya dauke da makami mai suna George Floyd.
Shugaban kasar ya bayar da umarnin ne ranar Juma'a da almuru bayan ya soke shirinsa na zuwa wurin buga wasan kwallon gora dinsa da ke Bedminster, a New Jersey, inda ya wallafa sakon Twitter da ke cewa zai zauna a Washington DC domin ya "tabbatar an bi DOKA da ODA".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Dokar ta ce: "Da dama daga cikin masu tarzoma, da masu fasa kantuna, da masu tsattsauran ra'ayi wadanda suka bayar da goyon baya kan wannan aika-aika, sun fito fili sun goyi bayan ra'ayoyi irin na Markisanci - wanda yake kira da a rusa tsarin gwamnatin Amurka."
An zargi masu zanga-zangar da "cikakkiyar jahiltar tarihinmu".
Dokar ta bayar da misali kan yadda kwanakin baya masu zanga-zangar suka hari wani gunki da ke San Francisco wanda tsohon shugaban Amurka Ulysses S Grant, ya mallaka kafin ya zama Kwamadan Soji inda ya yi nasara a kan wata kungiya da ke cinikin bayi lokacin Yakin Basasa, da kuma wani gunki a Madison, Wisconsin, na wani dan ci-rani wanda ya yi yaki don ganin hadewar kasar, da kuma wurin tunawa da Amurkawa bakaken fata da ke Boston.
"Daidaikun mutane da kungiyoyi suna da damar yin zanga-zangar lumana kan cirewa ko gina mutum-mutumi," a cewar dokar shugaban kasar.
"Amma babu wani mutum ko kungiya da take da damar lalatawa, ko cire mutum-mutumi da karfin tsiya."
Shugaban kasar ya bayar da misali da dokar da ta amince a yi daurin shekara goma a gidan yari ga duk mutumin da aka samu da laifin lalata kayan gwamnatin tarayya.
Shugaban kasar ya yi gargadin cewa za a dakatar da kudin gudanarwar duk rundunar 'yan sanda da ta gaza hana rusa ko lalata mutum-mutumin

Asalin hoton, Getty Images

Karin labarai kankisan George Floyd












