Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Twitter ya rufe shafuka 180 a China da Turkiyya da kuma Rasha
Kamfanin Twitter ya ce ya rufe wasu shafuka kimanin dari da tamanin mallakin gwamnati kuma mafi yawa daga China sai kuma sauran daga Turkiyya da Rasha.
Kamfanin ya ce ana amfani da shafukan wajen kai wa masu suka hari da yada labarai marassa tushe.
Twitter ya kuma ce ya bankado wasu shafukan da dama da ake amfani da su ta irin wannan fuska.
A cewar kamfanin sakonnin da ake wallafawa a shafukan sun fi mayar da hankali kan labaran da suka dace da jam'iyyar kwamunisanci da kuma yadda take tafiyar da batun annobar korona.