Minneapolis: An kori 'yan sanda huɗu daga aiki saboda kashe baƙar-fata a Amurka

Zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gudanar da zanga-zanga a Minneapolis

Magajin birnin Minneapolis da ke Amurka ya kore 'yan sanda hudu daga aiki wadanda ake zargi da sanadin mutuwar wani mutum bakar- fata bayan sun kama shi.

A hotunan bidiyon da ganau suka nada a ranar Litinin, an ji mutumin, wanda yake da kimanin shekara 40, yana ihu yana gaya wa daya daga cikin 'yan sanda wanda ya danne shi da gwiwar kafarsa cewa "ba na iya numfashi."

Magajin birnin, Jacob Frey ya yi Allah-wadai da abin da ya faru wanda ya bayyana a matsayin babban kuskure, sannan ya ce kasancewar mutum bakar-fata a Amurka ba laifin kisa ba ne.

Dan sanda

Asalin hoton, DARNELLA FRAZIER

Wannan lamari ya tuna wa mutane abin da ya faru da wani bakar-fata mai suna Eric Garner, wanda ya mutu lokacin da aka tsare shi a shekarar 2014.

An shake wuyan Garner da wani karfe inda ya rika cewa "Ba zan iya yin numfashi ba" kusan sau goma sha biyu.

Wannan kalami nasa ya zama wani furuci da masu fafutuka suka rika yi a wajen zanga-zangar kyamar cin zarafin da 'yan sanda suke yi wa bakaken-fata a Amurka.

Bakar Fata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bakar fata na ganin cewa ba a mutuntasu a Amurka