Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Afirka za ta dauki lokaci mai tsawo wajen yakar cutar
- Marubuci, Andrew Harding
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent, BBC News
Na shafe kusan dare daya ina bin wasu 'yan sandan Afirka ta Kudu a daidai lokacin da suke shawagi da dare a titin Alexandra da ke a Johannesburg.
Na shiga damuwa ƙwarai a wannan lokaci.
Duk bayan minti daya ko kuma wani lokaci, 'yan sandan kan tsayar da motarsu - jama'a kuma su yi da gudu suna ihu - su kuma 'yan sandan su kama daya ko biyu su jefa bayan mota.
Wata mata ba ta sanya takunkumi ba suka kama ta, in ji wani dan sanda. Wani kuma yana sayar da taba sigari wadda aka yi fasa-kwabrinta.
Mutane da dama na tsaye liƙe da juna, sai dai baza a iya tantance ko su wane ne ba saboda duhu.
Rashin gaskiya a jihar
Lamarin gaba daya ya tayar da hankali - a zahiri take karya doka ne.
Amma a lokacin da, ina tunani na daban dangane da yadda dare ke kasancewa a layin Alexandra, ba wai tunanin ɗabi'ar 'yan sanda ba, amma martanin da jama'ar wurin garin ke mayar wa.irin wahalar da mutanen wurin ke sha/
Su gudu, idan aka kama su bayar da kansu cikin sauki.
Na yi tunanin yadda waɗanda ba su da gata za su iya kalubalantar gwamnatin ƙasa.
Na ga hakan sau da dama, a nan Afirka ta Kudu - da kuma wasu kasashe na duniya a wasu nahiyoyin.
Na ji wani labari daga kusan mutane biyu kan wasu waɗanda aka kai 'yan uwansu asibitin gwamnati saboda suna "ciwon ciki," ko kuma "mura" sai dai kawai bayan kwanaki a ce sun mutu.
Hakan na nufin jama'a da dama na kallon 'yan sanda da ma'aikatan lafiya ba a matsayin wadanda za su ceci ran mutum ba sai dai wata ma'ana daban.
Akwai ce-ce-ku-cen da ake yi a farkon ɓullar korona kan cewa ba ta kama 'yan Afirka - duk da haka muna jin sanannun mutane irin su Shugaban Tanzania John Magafuli na ƙoƙarin kai mutane su baro.
Amma jama'a da dama da na tattauna da su musamman a ƙsashen da ba su da galihu sun nuna dagewarsu kan cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa sun kare kawunansuda kuma iyalensu daga wannan cuta ba sai sun jira gwamnati ba.
Afirka ta dauki matakan da suka dace
Wannan nahiya ce wadda za a iya cewa tarin lala (TB) da cutar HIV da Malaria na ci gaba da yin kisa duk da kokarin inganta bangaren lafiya - miliyoyin mutane na mutuwa a duk shekara.
Gwamnatoci da dama a fadin nahiyar sun yi iya yinsu wajen ganin cewa sun shawo kan manyan cutuka irinsu Ebola da korona.
Shiyasa ba su yi wata-wata ba wajen hanzartawa da daukar matakai a farkon ɓarkewar cutar.
A daidai lokacin da wasu ƙasashe ke ganin cewa cutar ba za ta iya yin komai garesu ba har suka bar filayen jiragensu a buɗe, ƙasashen Afirka na can na ƙokarin saka dokar hana fita tare da ƙoƙarin bayar da horo ga tarin jami'an kiwon lafiyarsu.
An yi jinkiri ko an shawo kanta kan lokaci?
Amma tambayar a yanzu ga Afirka ta Kudu da sauran kasashen nahiyar Afirka ita ce ko tunanin da kasashen ke yi na cutar kan iya yin illa garesu zai sa su ci gaba da yaƙar cutar kamar yadda suka faro.
Hujjoji da aka samu daga Najeriya zuwa Sudan ta Kudu da wasu kasashe bayan nan na nuna cewa kasashen sun yi jikiri a maimakon su shawo kan cutar.
Hasashen da masana suka yi na baya-bayanan nan a Johannesburg ya nuna cewa cutar za ta kashe sama da 'yan Afirka ta Kudu 40,000 zuwa tsakiyar watan Yuli.
Illolin dokokin kulle suka yiwa tattalin arziƙi na ƙoƙarin fito da halin da gwamnatoci suka shiga musamman waɗanda ba 'yan gaban goshin ƙasashen yamma bane.