Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Har yanzu ina mummunan mafarkin gidan yarin Saudiyya'
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Kano
A ranar 14 ga watan Mayu na 2020 ne Zainab Aliyu ta cika shekara guda cif da komawa mahaifarta Kano daga kasar Saudiyya bayan an tsare ta bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Gwamnatin Saudiyya ta kama Zainab ne tun a Disamban 2018 lokacin da ta je kasar tare da mahaifiyarta da 'yar uwarta domin gudanar da aikin Umrah.
Bayan an shafe lokaci mai tsawo ana tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriya da kuma Saudiyya, a karshe an wanke Zainab daga dukkanin zarge-zargen da aka yi mata na safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar Saudiyya.
Zainab ta shaida wa BBC cewa har yanzu tana mafarkai masu tayar da hankali idan tana barci, a cewarta sai ta rika jin tamkar tana cikin gidan yari ne amma duk lokacin da ta farka takan gode wa Allah don ganin a zahiri tana gida cikin dangi da mahaifa.
Ta bayyana cewa ba a azabtar da ita ba lokacin da take zaman gidan yari wanda hakan ya sa har ta san wasu da suka zauna tare kuma a yanzu tana matukar kewarsu.
Ta shaida cewa babban abin da take kewa shi ne karatun Qur'ani da suke yi a cikin gidan yarin inda har ta hardace ayoyi masu yawa daga littafin mai tsarki.
''Abin da ya faru a Saudiyya a kullum yana raina, kuma yanzu da shekara daya ta matso, ina yawan tunawa, da a ce na mutu a can fa?"
A halin yanzu Zainab ta kammala karatunta a jami'ar Maitama Sule da ke Kano kuma ta shaida wa BBC cewa ba ta shirya yin aure yanzu ba.
''Ina fatan yin aure amma a yanzu ban shirya ba tukunna.''
Zainab ta bayyana cewa tana fatan shari'ar da ake yi ta wasu ma'aikatan filin jirgin Aminu Kano da aka zarga da kulla mata sharri za a kammala ta cikin gaggawa domin yanke musu hukuncin da ya dace.
Kafin sakin Zainab daga Saudiyya wasu dalibai a Kano sun gudanar da zanga-zanga don neman a sake ta.
Tun kafin gudanar da zanga-zangar, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari'a Abubakar Malami ya shiga maganar Zainab Aliyu domin ganin an sake ta.
Rahotanni da dama a shafukan intanet na nuna cewa akwai 'yan Najeriya masu yawa da aka yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya kan laifuka daban-daban.