Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Masana kimiyya sun rude kan illar rikidar kwayar cutar korona
- Marubuci, Daga Rachel Schraer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai aiko da rahotanni kan kiwon lafiya
Masu bincike a Amurka da Burtaniya sun gano daruruwan hanyoyin da cutar dake harfar da korona take iya rikida.
Sai dai har yanzu babu ko hanya daya da ta bayyana me hakan zai haifar game da bazuwar cutar cikin mutane da kuma yadda tasirin allurar riga-kafinta za ta kasance.
Cutuka na rikidewa - wannan ne abin da suke yi.
Tambayar anan ita ce, wacce ce daga cikin rikidar ke yin wani abu domin sauya hadari da kuma yadda ake kamuwa da cutar?
Binciken da ya gabata daga Amurka ya ce daya daga cikin rikidar da cutar take - D614G - zai iya zama ya mamaye ko'ina a nan gaba kuma ya kara girman hadarin kamuwa da cutar.
Har yanzu dai wasu masana kimiyyar ba su bibiyi wannan binciken ba kuma ba a wallafa shi ba a hukumance.
Masu binciken, daga dakin bincike na Los Alamos da ke New Mexico, na bibiyar yadda rikidewar cutar ke karuwa tare da ba ta wani salo na daban.
Sun kuma fahimci wani abu a tare da wannan cutar daya game da yadda take rikidewa da kuma bunkasa cikin gaggawa - amma har yanzu ba a kai ga gano irin tasirin da za ta iya haifarwa ba.
'Rikidar ba wani mummunan abu ba ne'
Masu binciken sun bibiyi bayanan da aka tattara daga marasa lafiya a Sheffield da ke Burtaniya.
Sun kuma gano mutanen da ke dauke wannan nau'in cutar suna da adadi mai yawa na cutar a samfurinsu, ba su dai gano dalilin da ya sa rashin lafiyar mutanen ta yi tsanani ba - kila ko don sun dade a asibiti ne.
Wani karin binciken daga jami'ar Landan ya gano sauye-sauye 198 da ke faruwa game da wannan cuta.
Daya daga cikin wadanda suka yi binciken shi ne Farfesa Francois Balloux, rikidar a kan kanta ba wani mummunan abu ba ne, babu kuma abin da za a iya cewa kan SARS-Cov-2 ko ana tsammanin rikidewarta cikin gaggawa ko a hankali.
"Ya zuwa yanzu, ba za mu iya cewa ko SARS-CoV-2 tasirin kisanta na raguwa da kuma yadda ake kamuwa da ita."
Wani binciken daga jami'ar Glasgow, wanda ya yi nazari kan rikidewar, ya ce wannan sauye-sauyen ba sa kara wani hadari ga cutar. sun kuma karkare binciken da cewa nau'i daya ne kawai na cutar a yanzu yake zagayawa.
Bibiyar kananan sayin da cutar ke haifarwa na da amfani domin samar da allurar riga-kafi ga duniya.
Dauki misalin cutar Spanish flu: tana rikida cikin gaggawa ta yadda akwai bukatar rika bunkasa allurar riga-kafinta duk shekara domin kauda tasirin da take haifarwa lokaci zuwa lokaci.
Samar da magani
Mafiya yawan alluran riga-kafin da ake samarwa na korona na kokarin rage karuwar cutar ne - manufar ita ce samarwa da jiki wani sauyi na daban da zai taimaka wajen yakar duka cutar.
Amma matukar yadda cutar ke karuwa yana sauyawa, to tasirin riga-kafin da aka samar zai kasance ba shi da karfi.
Wadannan duka bayanai ne na fatar baki, Masana kimiyya har yanzu basu da cikakkun bayani kan menene ke janyo rikidewar wannan cuta da kuma manufarta.
Dakta Lucy van Dorp, wacce ita ce mataimakin wanda ya wallafa binciken jami'ar Glasgow ya ce, samun damar bibiyar tsatson cutatukan masu yawa zai iya zama abu mai muhimmanci wajen kokarin samar da maganin cutar.
Haka kuma, ta shaida wa BBc "Ina son asali, amma sai dai kawai muyi magana kansu da baki."