Tarihin Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ila

Rano Emirate Council

Asalin hoton, Rano Emirate Council

Bayanan hoto, Margayin na fama da ciwon hawan jini
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Asabar 2 ga watan Mayu ne Allah Ya yi wa Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila rasuwa a asibitin Nasarawa da ke Kano.

Tuni aka yi jana'izarsa a garin Rano a yammacin ranar.

Alhaji Tafida Abubakar Il ya rasu ne bayan gajeriyar jinya, yana da shekara 74, kamar yadda Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano da Bunkure kuma Turakin Rano ne ya tabbatar wa BBC labarin rasuwar.

Mai magana da yawun Masarautar Rano Wali Ado ya ce Sarkin ya yi jinyar kwana biyar ne, inda aka kai shi asibiti a ranar Juma'a.

Yana daga cikin sarakuna hudu masu daraja ta daya na sababbin masarautun jihar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira a bara.

Wali Ado ya ce dama Sarkin yana da cutar hawan jini da ciwon suga da ke taso masa lokaci-lokaci.

Me ya faru bayan jana'izarsa?

A ranar Lahadi ne Masarautar Rano ta yi karin bayani kan wani bidiyon gawa da ke yawo a kafofin sada zumunta na intanet da aka alakanta da Sarkin Rano da Allah Ya yi wa Rasuwa.

Wali Ado ya ce bidiyon da ke yawo ba na gawar Sarkin ba ne domin jami'an lafiya ne suka yi masa jana'iza.

Fadar masarautar Rano da ke jihar Kano a Najeriya ta ce tana jiran sakamakon gwajin da aka yi wa marigayin domin tabbatar da ainihin abin da ya yi ajalinsa.

Kakakin fadar ya ce yanayin mutane da suka kawo gawar mai martaba akwai alamomin da ke nuna akwai matsalar.

''Yanayin Jami'an lafiya da suka kawo gawar da binnewar cikin gaggawa gaskiya ba a saba ganin jana'iza irin hakan ba''

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

Wannan bidiyon na nuna Sarkin Rano Tafida Abubakar Ila yayin da yake isa filin wasa na Sani Abacha a birnin Kano ilokacin da za a rantsar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa a karo na biyu.

Wane ne Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ila?

An haifi Dr Tafida Abubakar Ila garin Rano jihar Kano a shekara ta 1945.

Mahaifinsa shi ne Isau (Mal Tsoho) daya daga cikin 'ya'yan Sarkin Rano Ismaila, mahaifiyarsa kuma ita ce Hajia Zainab 'yar Amadu Sarkin Chirin Mashi da Binta (Intu) jikar Sarkin Kano Maje Karofi.

Ya Halarci makarantar Elementary ta garin Kibiya a shekara ta 1955 zuwa 1959, Rano Senior Primary School daga 1959 zuwa 1961 sai sakandiran Gwamnatin Birnin Kudu daga 1963 zuwa 1967.

Ya tafi makarantar Institute of Social Work wacce take a Iferu jihar Ogun daga 1973 zuwa 1978 sai kuma Jami'ar Bayero Kano a 1991.

Marigayi Maimartaba Sarkin Rano ya yi aiki a kamfanin inshora na Royal Exchange Assuarance a Kano a shekara ta 1967 zuwa 1968.

Ya kuma yi aiki a ma'aikatu daban-daban na gwamnatin Kano kamar Ma'aikatar Gona, lafiya da jin dadin jama'a. Haka kuma a shekarar 1991 zuwa 2000 ya yi aiki a ma'aikatar kidaya ta kasa.

An yi masa sarautar Barayan Kano kuma Hakimin Bunkure daga shekarar 2000 zuwa shekara ta 2004, sannan aka nada shi Sarkin Rano, Hakimin Rano daga 2004 zuwa 2019.

A shekara ta 2019 aka daga likafarsa zuwa Sarkin Masarautar Rano Mai Daraja ta Daya.

Marigayi Mai martaba Sarkin Rano ya yi kwasa-kwasai da bitoci daban-daban. Haka kuma ya rike mukamai daban-daban a karamar hukuma kamar kansila da kuma mataimakin shugaban karamar hukumar Rano.

Dr Tafida Abubakar Ila ya kasance mutum mai sha'awar karance-karance da tafiye-tafiye da noma da kuma kiyon dabbobi.

Autan Bawo kamar yadda aka fi sanin sa ya rasu ya bar ata biyu da 'ya'ya 17, 12 maza, biyar mata.

Bayanai daga masarautar Rano