Coronavirus: 'Yan Afirka na fuskantar wariya a China

'Yan Afirka a China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai 'yan Afirka da dama a Guangzhou da ke hada-hadar kasuwanci

Ana bayyana fargaba kan zargin cin zarafi da hukumomin China a garin Guangzhou ke yi wa 'yan Afirka kan cutar coronavirus.

Ana zargin hukumomin na China da nuna kyama ga bakaken fata 'yan Afirka kan fargabar cewa suna yada cutar coronavirus a kasar.

Amurka ta yi gargadi ga 'yan kasarta bakaken fata su kaurace wa garin.

Wani karamin ofishin diflomasiyar Amurka ya ce 'yan sandan China sun ba gidajen sayar da abinci umarnin daina sayar da abinci ga 'yan Afirka.

Wasu mazauna Guangzhou 'yan Afirka sun ce ana ta korarsu daga gidajensu, yayin da kuma wasu suka ce ana korarsu a otel-otel.

Ma'aikatar harakokin wajen China ta amince cewa "akwai rashin fahimta da aka samu a wasu lokuta."

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Wasu rahotanni sun ce ana ta yi wa bakaken fata 'yan Afirka gwajin coronavirus, tare da killace su a gidajensu na tsawon mako biyu duk da cewa ba su nuna wasu alamun cutar ba.

Duk da cewa a China aka fara samun barkewar cutar, hukumomin China sun tsaurara matakai na dakile sake shigo da ita daga waje.

Akwai 'yan Afirka da dama a Guangzhou inda ake hada-hadar kasuwanci, wadanda ke zuwa saro kaya zuwa Afrika.