Wadanne tambayoyi kuke da su a kan Coronavirus?

coronavirus

Asalin hoton, Getty Images

Ana ci gaba da samun yaduwar cutar coronavirus a fadin duniya, al'amarin da yake tsayar da abubuwa cak tare da sanya fargaba a zukatan mutane kan irin barnar da annobar ka iya jawowa duniyar.

Ko a makon da ya gabata an samu kasashen Afirka da dama da suka sanar da bular Covid-19, yayin da wasu suka samar da karuwar alkaluman wadanda suka kamu da ita.

Seychelles, eSwatini, Namibia, da Guinea da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da Congo da kuma Equatorial Guinea ne kasashen da cutar ta bulla a karon farkon, Sai kuma kasashen Rwanda da Habasha da Kenya da DR Congo da masu dauke da ita suka karu.

Ku aiko da tambayoyinku kan abin da kuke so ku sani kan coronavirus, BBC kuma za ta gudanar da bincike tare da kawo muku cikakkiyar makala.

Ku sanya sunanku a kasa idan kuna son a wallafa tambayarku a cikin makalar.