Mutum na biyu da ya kamu da coronavirus a Najeriya ya warke

Ministan Lafiya a Najeriya, Osagie Ehanire, ya ce mutum na biyu da ya kamu da cutar coronavirus a kasar ya warke.

Ministan ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce dayan mai dauke da cutar dan kasar Italiya ya samu sauki kuma za a sallame shi daga asibitin da yake jinya a Legas makon gobe.

Ministan ya ce Najeriya ba za ta hana jirage ko mutane shiga da fita daga kasar ba, saboda yadda hakan ka iya shafar tattalin arzikin kasar.

Kwanan nan ne gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti don yin bincike kan tasirin annobar coronavirus ga tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma ce duka mutanen da suka yi mu'amala da shi sun gama duka gwaje-gwajen da suka dace.

Kazalika, an tabbatar ba sa dauke da cutar sannan suna iya ci gaba da rayuwarsu yadda suka saba.

A watan Fabrairu ne Najeriya ta samu mutum na farko da ya kamu da coronavirus - wani dan Italiya dan kasuwa da ya je kasuwanci Najeriya.