Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum na farko mai dauke da Coronavirus ya warke a Saudiyya
Saudiyya ta sanar da mutum na farko da ya warke daga cutar coronavirus daga cikin wadanda suka kamu.
Wata sanarwa daKamfanin Dillancin Labaran kasar na SPAya wallafa a shafinsa na intanet daga Ma'aikatar Lafiya, ta ce mutumin wanda dan kasar ne ya kasance a cibiyar killace marasa lafiya da ke babban Asibitin Qatif a yankin Gabashin kasar, kuma yana cikin halin lafiya a yanzu.
Sanarwar ta ce an kammala duk wasu gwaje-gwaje da ke da alaka da cutar tasa kuma an tabbatar da cewa ba ya dauke da ita ba.
Zuwa jiya Laraba akwai mutum 21 da ke dauke da coronavirus a kasarMa'aikatar ta nemi duk wadanda suka shiga kasar da su bayyana kasashen da suka je kafin Saudiyyar ta hanyar kiran wata lambar waya ta musamman.
Haka kuma Ma'aikatar Lafiyar ta karyata rahotannin da ke cewa an samu masu dauke da cutar har 600.
Sannan Saudiyya ta dakatar da tafiye-tafiye ga 'yan kasarta da mazauna kasar zuwa kasahse 39 da suka hada da kasashen yankin Turai yayin da aka samu karuwar masu dauke da coronavirus daga 21 zuwa 45, da suka hada da 21 a Makkah, kamar yadda Jaridar Saudi Gazette ta wallafa.
Tun a makon da ya gabata Saudiyya ta sanar da dakatar da mazauna kasar daga yin aikin Umrah na wucin gadi a kokarinta na hana yaduwar Coronavirus.
Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar ta fitar ta ce an dauki wannan matakin ne domin bayar da hadin kai ga hukumomin lafiya na duniya don shawo kan cutar.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Cikin Gidan ya danganta daukar matakin da kaguwar gwamnatin Saudiyyan na goyon bayan kokarin da duniya ke yi, musamman ma manyan hukumomi irin Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, na hana yaduwar cutar.