WHO ta ce 'Coronavirus ta kai matsayin zama annoba a duniya'

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce cutar coronavirus ta kai wani matsayi na zama annoba a duniya.

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya, Dr. Tedros Ghebreyesus ne ya bayyana girman barazanar da cutar corona a duniya inda ya ce ta kai wani "gagarumin matsayi" da za ta zama "annobar duniya".

Kalamansa na zuwa ne yayin da kasashe a fadin duniya ke ci gaba da fafutukar kare kwayoyin cutar daga kara bazuwa.

Iran da Italiya sun zama manyan wuraren da cutar ta fantsama, inda mutanen da suka fito daga kasashen ke ci gaba da baza kwayoyin cutar.

Iraniyawa da yawa ne suka harbu da cutar, kuma na baya-bayan nan shi ne mataimakiyar shugaban kasa kan harakokin mata da iyali Masoumeh Ebtekar.

"Abin da ke faruwa a sauran kasashen duniya ne yanzu babbar damuwarmu," in ji Dr Tedros.

A duniya, sama da mutum 80,000 a kasashe kusan 50 ke dauke da cutar. Kusan mutun 2,800 suka mutu, yawancinsu lardin Hubei na China.

A daya bangaren kuma darajar hannayen jarin duniya ta fadi saboda yadda matakan takaita tafiye tafiye da kasashe ke yi wanda ke shafar harakokin kasuwanci.

Me Hukumar Lafiya ta ce?

Dr Tedros ya bukaci gwamnatocin duniya su gaggauta daukar matakan dakile yaduwar cutar.

"Muna cikin mawuyacin hali inda barkewar cutar za ta iya bulla a kowane bangare bisa ga yadda muka tunkare ta."

Wannan ba lokaci ba ne na faragaba ba, wannan lokaci ne na daukar matakin dakile cutar da kare rayuka," in ji shi.