An kai gwamnan CBN na bogi gidan yari a Najeriya

Asalin hoton, CBN/FACEBOOK
Wata kotu a Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekaru uku ga Nwalozie Onyebuchi Julius, wanda a kwanakin baya ake zarginsa da fakewa a matsayin gwamnan Babban Bankin Najeriya wato Godwin Emefiele.
Mai shari'a Agatha Anulika Okeke ta Kotun Tarayya a garin Uyo reshen jihar Akwa Ibom ce ta yanke hukuncin, inda ta ce zai shafe shekaru uku a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.
A kwanakin baya ne dai hukumar EFCC a Najeriya ta maka Mista Onyebuchi a gaban kotu kan zarginsa da yin sojan gona da sunan gwamnan CBN tare da yin damfara da ta kai ta naira miliyan 4.5.
A Disambar bara ne hukumar EFCC reshen jiyar Uyo ta samu bayanan sirri kan almundahana da ake yi a shafukan intanet a jihar, wanda hakan ya kai ga kama Mista Onyebuchi.
Jim kadan bayan Mista Onyebuchi ya shiga hannu, ya amince da aikata laifin da ya yi, haka zalika a wata kwamfutarsa kirar HP da aka yi bincike a kanta, an samu hujjoji da suka nuna ya aikata laifukan da suka hada da damfara da wasu laifuka da ake yi a intanet.







