Hotunan ziyarar da Sheikh Dahiru Bauchi ya kai wa Buhari

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Bauchi, ya kai wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara ranar Lahadi.

Hotunan da mai taimaka wa shugaban kasar kan kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter sun nuna shugaban kasar da Sheikh Bauchi da dansa da ma wasu 'yan rakiyarsa a fadar Aso Villa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Ko da yake ba a fadi dalilin kai ziyarar ba, amma malamin ya je fadar shugaban Najeriyar ne a yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da ta'azzara a sassan kasar.

Malamin ya yi shuhura wajen gaya wa shugabanni gaskiya.