An kashe sojojin Amurka a Afghanistan

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Sojojin Amurka biyu da kuma daya na Afghanistan ne aka kashe a wani hari a gabashin kasar Afghanistan.
Mutm tara aka jikkata a harin na yankin Nangarhar a ranar Lahadi.
"Rahotonni sun nuna cewa wani mutum ne sanye da kakin sojan Afghanistan ya bude wa sojojin kasashen biyu wuta da wata mashinga," in ji Kanar Sonny Leggett, mai magana da yawun rundunar sojin Amurka.
Har yanzu akwai sojojin Amurka 13,000 a Afghanistan tun bayan da ta kutsa kasar a shekarar 2001, inda ta tumbuke gwamnatin kungiyar Taliban.
"Muna ci gaba da tattara bayanai game da harin amma har yanzu ba mu san dalilin da ya sa aka kai shi ba," Leggett ya bayyana a wata sanarwa.
An kashe maharin da ya kai harin yayin artabun, kamar yadda wani dan majalisar yankin, Sohrab Qaderi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ma'aikatar tsaro ta Afghanistan ta ce wata tawaga tana ci gaba da bincike kan lamarin tare da ta Amurka a Nangarhar.







