'Jawabin Trump labarin kanzon-kurege ne'

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi jawabin shekara-shekara ga Amurkawa a gaban majalisar kasar kan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasar bayan jagorantar kasar da yayi na shekara uku.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin jawabin da ya yi wa Amurkawa a gaban zauren majalisar kasar da dukkan 'yan majalisa na wakilai da na dattawa suka halarta.
A al'ada, shugabannin A,murka kan gabatar da irin wannan jawabin ne domin sanar da kasar muhimman abubuwa da suka shafi kasar kamar tattalin arziki da shigar kasar yaki.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana abubuwan da ya ce a gurinsa su ne ci gaban da ya samu bayan jagorantar Amurka da yayi na shekara uku.
Kuma ya bayyana haka ne a yayin jawabi ga kasa da ya yi wa Amurkawa a gaban dukkan 'yan majalisar kasar.
Mr Trump ya zabi yin wannan jawabin ne kwana daya kafin majalisar dattawan Amurka ta fara zaman wanke shi daga tuhumar aikata ba daidai ba da ya janyo majalisar wakilai ta tsige shi a watan Disambar bara.
A lokacin jawabin, ya bayyana habakar tattalin arziki da karuwar ayyukan yi da kuma cikin abubuwan da ya ke alfahari da su.
Shugaba Trump: "Rashin aikin yi tsakanin Amurkawa bakaken fata da 'yan Latino ya yi faduwar da ba a taba gani ba a tarihi. Kuma a cikin shekara 70 da suka gabata, ba a taba samun yawan mata masu aikin yi ba kamar a lokacin mulki na, inda a bara kawai mata ne suka sami kashi 72 cikin 100 na dukkan sabbin ayyukan da aka samar."
Shugaban ya kuma ce bangaren kera-kere na farfadowa, ya kuma tabo rikicin kasuwanci da ke tsakanin Amurka da China, wanda yayi ikirarin cewa Amurka ta sami galaba kan Chinar ne saboda kwarewar da ya nuna na jagorantar tattaunawar da aka yi domin warware rikicin.

Asalin hoton, AFP
Trump da Pelosi sun kara
Sai dai wani abu ya ja hankulan wadanda suka halarci zaman.
A lokacin da Mista Trump ya shiga zauren majalisar, kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ta mika ma sa hannu domin su gaisa, amma sai Mista Trump ya yi kamar bai gan ta ba, matakin da bai bai wa kowa mamaki ba.
Sai dai ita ma kakakin ta rama cin fuskar da yayi ma ta, domin bayan da ya kammala jawabin nasa, sai ta mike tsaye, ta tattara takardun jawabin da shugaba Trump ya gabatar kuma ta kekketa su ta wa watsar da su kowa na kallo.
Martanin jam'iyyar adawa ta Democrat
'Yan jam'iyyar Democrat sun ce jawabin nasa cike yake da alfahari, amma babu kwararan matakai a kasa.
Madeiliene Dean, 'yar majalisar wakilai daga jihar Pensylvania ta mayar wa shugaban da martani.
"Jawabin nasa cike yake da abubuwan da suka yi hannun riga da ayyukan da ya shafe shekara uku yana yi. Ya rika rusa dangantakarmu da al'umomi tsiraru na kasar nan, ya kuma sha taka dokokin da aka kafa domin kare muhalli. Ya kuma lalata tsarin ilmi, amma sai ga shi yau yana magana kan yadda harkar ilimi ke kara sukurkucewa."
Ta kuma bayyana cewa jawabin shugaban cike yake da labaran kanzon kurege, "da karairayi", wanda ta ce da kyar ta iya hadiye kalaman nasa.











