Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kenya: An samar wa mata kofin yin fitsari don hana kamuwa da cuta
Wata mata 'yar kasar Kenya ta samar da wata mafita ga masu fama da irin cututtukan da ake kamuwa da su bayan amfani da bandakunan da ba su da tsafta.
Njeri Muthaka tana sayar da kofunan da ke taimaka wa mata yin fitsari a tsaye, ba tare da sun tsuguna ba don kare su daga zama kan shadda mara tsafta da za su iya daukar kwayoyin cuta.
Ms Muthaka ta shaida wa BBC Swahili cewa ta sayo kofunan yin fitsarin ne daga wata kasa, bayan da ta yi fama da cututtukan da suka shafi al'aura da mafitsara ba sau daya ba ba sau biyu ba.
Bayan da ta yi amfani da kofin ta kuma ga muhimmancinsa wajen hana ta sake kamuwa da cutar, sai ta yanke shawarar sayar da kofunan.
Likitoci sun yi amanna cewar kofin fitsarin zai rage kamuwa da cututtuka.
Wani likita Chris Obwaka ya ce: "Idan har ba kya zama a kan shadda ta gama-gari don yin fitsari, hakan zai iya rage hadarin kamuwa da cututtuka. Amfani da kofin zai taimaka sosai."
Sai dai mazan Kenya na cewa amfani da kofin ya kauce wa tsarin al'adunsu.
"Hakan ya sabawa al'ada saboda babu kyau mace ta yi fitsari a tsaye," kamar yadda Simon Baraza ya shaida wa BBC Swahili.
Ana sayar da kofin fitsarin a kan dala biyu, kuma Ms Muthaka ta ce ta sayar da kusan 400 a kasashen Gabashin Afirka.