Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba mu amince da shirin Trump ba - Falasdinawa
Falasdinawa sun yi watsi da tayin da sabon shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya, tare da bayyana shi a matsayin mai cike da tuggu.
Shirin ya bai wa Falasdinawa da 'yan Isra'ila damar ayyana birnin Jerusalam ko Kudus a matsayin nasu, wato kowacce kasa za ta dauki wani yanki na birnin, sai dai yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan zai kasance mallakin Isra'ila ita kadai.
Da yake mayar da martani game da sanarwar ta ranar Talata, shugaba Mahmoud Abbas na Falasdinu ya ce birnin Kudus ba na sayarwa ba ne.
''Dukkanin hakkokin mu ba na sayarwa bane, ba kuma na saryarwa ba'', inji shi.
A ranar Talatar nan, dubban Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga a Zirin Gaza, yayin da dakarun sojin Isra'ila suka karfafa tsaro a Gabar Yammacin Kogin Jordan.
Surukin Shugaba Trump Jered Kushner ne ya tsara kudin wanda ke da manufar warware dadaddiyar tsamar da ke akwai tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
Da yake magana kusa da Firai Ministan Israila Benjamin Netanyahu, Shugaba Trump ya ce wannan ce dama ta karshe da gwamnatinsa za ta bai wa Falasdinawa don wanzar da zaman lafiya a yankin.
Rahotanni sun ce, Mista Netanyahu na shirin ci gaba da bayyana kashi 30 cikin dari na yankin Gabar Yammacin Jordan da kasarsa ta mamaye, tare da jefa kuri'ar majalisar ministoci a ranar Lahadi.
Isra'ila ta zaunar da Yahudawa kimanin dubu 400 a yankin da karin wasu 200,000 a Gabashin Kudus. Ana ɗaukar ƙauyukan ba bisa ƙa'ida ba a ƙarƙashin dokokin ƙasa, ko da yake Isra'ila ta musanta hakan.
Me Abbas ya ce?
Da yake magana a ranar Talata, ya ce "abu ne mai wuya ga kowane Bafalasdine, da Balarabe da Musulmi ko Kirista su karbi" ƙasar Falasdinu ba tare da Kudus a matsayin babban birninta ba.
"Mun fada sau dubu, a'a, a'a, a'a," in ji shi. "Mun yi watsi da wannan yarjejeniyar tun farko kuma ra'ayinmu ya yi daidai."
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, wadda ke iko da Zirin Gaza, ita ma ta yi watsi da yarjejeniyar wadda ta ce tana nufin "shawo kan ayyukan Falasdinawa".
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tana ci gaba da kokarin warware matsalolin kasashen biyu bisa la'akari da yarjejeniyoyin da aka shimfida kafin 1967, lokacin da Isra'ila ta kwace Gabar Yammacin Jordan da kuma Zirin Gaza.
Shi kuma Netanyahu fa?
Ya bayyana shirin na Shugaba Trump a matsayin wanda ba a taba yin irin sa ba a wannan karni.
''Isra'ila ba za ta yi wasa da wannan dama ba'', in ji Mista Netanyahu.
''Allah ya wanzar mana da zaman lafiya da tsaro'', inji shi.
Menene martanin kasashen duniya?
Mai magana da yawun shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kiran samar da yarjejeniyar zaman lafiya bisa doron sharuddan da ta cim ma a baya, da kuma dokokin kasashen biyu.
Kungiyar kasashen Larabawa ta ce, za ta kira wani taron gaggawa a ranar Assabar mai zuwa.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Dominic Raab ya yi kira ga Falasdinawa su nazarci shirin, sannan su nuna wa duniya ko za su sake komawa kan teburin sulhu.
Wadanne muhimman abubuwa shirin na Trump ya kunsa?
·Amurka za ta bai wa Isra'ila iko da Gabar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da matsugunan Yahudawa da kuma bangare mafi rinjaye na kogin Jordan.
·Zai nunka fadin kasar da Falasdinawa ke da ita, tare da ba su ikon kafa babban birni a Gabashin Kudus, inda Shugaba Trump ya ce Amurka za ta bude ofishin jakadancinta.
·Birnin Kudus zai kasance babban birnin Isra'ila, sai dai Falasdinawa sun ce suna son yankin gabashin birnin ya kasance hedikwatar babban birninsu da zarar Kudus ya zama nasu.
·Babu wani Bafalasdine ko dan Isra'ila da za a tayar daga gidansa, don haka kowa zai ci gaba da kasancewa a inda yake.
·Isra'ila za ta yi aiki da Jordan, don tabbatar da matsayi na musamman na Masallacin Kudus, da kuma wuri mafi tsarki ga su kansu Yahudawa wato Dutsen Haikali ta yadda kowa zai rika gudanar da harkokin addininsa cikin aminci.
·Yankunan da aka bai wa Falasdinawa a taswirar yankin za su ci gaba da kasancewa a bude, ba tare da mamaya ba har nan da shekaru hudu, ta yadda Falasdinawan za su sami damar nazartar yarjejeniyar, kana su sasanta da Isra'ila, don cim ma ka'idojin zama tare.
Kazalika Shugaba Trump ya ce ba za a yanki wani yanki na Gabar Yammacin Jordan ba bisa wannan yarjejeniya.
Menene asalin al'amarin ?
Falasdinawa sun yanke alaka da gwamnatin Mista Trump tun a shekara ta 2017, bayan matakinsa na ayyana Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila tare da bude ofishin jakadancin kasar sa a can.
Tun daga wannan lokacin ne Amurka ta daina bai wa Falasdinu dukkanin wani taimako da take ba ta.
A watan Nuwamban 2019 ne sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi watsi da matsayin kasar na baya, na cewa matsugunan da Yahudawa ke zaune a cikinsu a Gabar Yammacin Jordan ba su dace da dokar kasa da kasa ba.
Me ake fuskanta a yanzu ?
Dukkanin tashe-tashen hankulan da ake yi a Gabas Ta Tsakiya tsakanin Falasdinawa da Isra'ila ya zamo mafi rikitarwa, duk kuma da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi a 1993, rikicin ya ci gaba da kankama.
Birnin Kudus
Kasashen Israila da Falasdinu na karajin cewa birnin nasu ne, Isra'ila wacce ta mamaye Gabashin Kudus a 1967 ta dauki birnin a matsayin nata, amma Falasdinawa suma sun jaddada cewa birnin nasu ne, akwai a kalla Falasdinawa 350,000 da ke zaune a yankin gabashin birnin.
Kasancewar Falasdinawa
Falasdinawa na son 'yancin cin gashin kai, tare da hada musu da Yankin Gabar Yammacin Jordan da kuma Zirin Gaza da Gabashin Kudus, Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kafe a kan cewa lallai ne birnin ya zamo na bangarorin biyu.