Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bola Tinubu ya ce ba a fahimci shirin Amotekun ba
Jagoran jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ya nemi zama da gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma da kuma Ministan Shari'a na kasar, Mallam Abubakar Malami, don tattaunawa kan batun Amotekun, inda ya ce akwai matsalar rashin fahimtar tsarin.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Bola Tinubu da aka aike wa manema labarai, ya ce kafa kungiyar tsaron ta Amotekun sam-sam ba barazana ba ce ga kasar tun bayan da gwamnonin yankin suka kafa ta, a kokarinsu na magance matsalar tsaro a jihohinsu.
A cewar sanarwar "batun Amotekun ya karade ko ina kuma ya ja hankalin kafafen yada labarai, ya shafi yadda gwamnatoci za su taimaka wajen bai wa al'umominsu tsaro.
"Wannan abun damuwa ne sai dai kuma an sanya siyasa cikinsa."
Tsohon gwamnan na Legas ya kuma ce "wadanda suke ikirarin gwamnatin kasar na neman dankwafar da Kudu Maso Yamma ne, kawai ra'ayinsu suke fada."
A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta soke kungiyar tsaro ta Amotekun da wasu jihohin shiyyar kudu suka samar.
Tun bayan daukar wannan mataki dai, jama'a a kasar ke tofa albarkacin bakinsu game da lamarin inda wasu ke ganin matakin wani koma baya ne, kuma yana iya zama matsala a kasar nan gaba.
An yi wa sanarwar mai dauke da sa hannunsa taken "Tattaunawa game da Amotekun"
"Akasarin mutane ba su fahimci Amotekun ba amma kuma suna ganin babu wani alfanu a tattare da shi.
Ka tambayi wadanda suke sukar Amotekun. Su ma ba su san komai ba game da ita. Suna sukar abin ne kawai saboda 'yan hamayya ne suka gabatar da tsarin ko kuma saboda suna ganin ba za su amfana da abin ba.""Yadda mutane ke yi wa batun mummunar fahimta ya nuna cewa akwai sauran aiki a gabanmu wajen gyara dimokradiyya.
"Ana ta ce-ce-kuce a kan batun a maimakon samar da maslaha wajen habaka tsaron cikin gida ba tare da an taba kundin tsarin mulkin kasa ba," in ji Jagaban kamar yadda ake kiransa.
Makomar Najeriya na cikin barazana
Ya ce makomar Najeriya na cikin barazana idan har haka jama'a za su rika tafiyar da sabanin da ke tsakaninsu.
"A wannan batun, ban ga aibu a sabanin ra'ayin da ake samu tsakanin gwamnonin kudu maso yamma ba wadanda suka kirkiri Amotekun da kuma Ministan Shari'a a matsayin jami'in tabbatar da dokar gwamnatin Najeriya.
"Akwai bukatar a samar da maslaha don magance matsalar a maimakon yi mata kwaskwarimaliya," a cewarsa.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnonin kudu maso yamma sun kafa kungiyar domin shawo kan matsalolin tsaro sannan su sauke nauyinsu na tabbatar da tsaro.
"Babu wanda za a zarga kan kokarin da suke na ganin sun sauke nauyinsu a matsayin gwamnoni." in ji sanarwar.
"Har zuwa yanzu, na zabi na yi shiru na kuma nazarci batun na Amotekun. Wadanda suke sukar abin sun yi haka ne ba wai saboda sun damu da Amotekun ko kuma mutanen da suke kokarin karewa ba ne.
"Sun yi haka ne da sanin cewa batun ya dauki hankalin jama'a."
"Idan har ni dan jagora ne na gaske a siyasance kamar yadda ake gani na, bai kamata na furta magana mara ma'ana ba. Akwai wadanda za su furta kalaman da ba su dace ba don janyo ce-ce-ku-ce."
"Ina fatan alheri ga Najeriya. Ina son al'ummar kasar, dukkansu.
"'Yan kasar sun shafe tsawon shekaru suna fuskantar kalubale da dama amma suke ci gaba da yin hakuri da fatan alheri.
"Ba zan yi watsi da irin mutanen ba ko kuma ba zan furta abin da zai taba zukatansu ba. Babban abin da na fi damuwa da shi shi ne walwalar mutanen."
"Sannan kuma ina bayyana ra'ayina kan wani batu bayan na gama tattara sahihan bayanai tare da yin nazarinsu."
Maslaha
Tinubu ya kuma ce a ganisa, za a iya kasa batun zuwa kashi uku da suka hada da;
- Alfanun Amotekun
- Tuntuba
- Shawarwari.