Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tunisia: An yanke wa mutum 8 hukuncin kisa kan harin bam
Wata kotu a kasar Tunisiya ta yanke wa mutum takwas hukuncin kisa ranar Juma'a bisa laifin kai harin da ya yi sanadiyyar kashe jami'an tsaro 12 a shekarar 2015 a kasar, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP.
Harin na ranar 24 ga watan Nuwamban 2015 wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa, ya halaka akalla mutum 12 a babban birnin kasar Tunus kuma ya raunata wasu 20.
Mataimakin mai shigar da kara Mohsen Dali ya shaida wa AFP cewa: "Kotun ta yanke wa mutum takwas hukuncin kisa wadanda aka zarga da kai hari kan motar bas ta dakarun fadar shugaban kasa."
Wasu mutum biyu kuma an yanke masu hukuncin shekara 10 a gidan yari, inda aka yanke wa daya hukuncin zaman gidan yari na har abada.
Wadanda aka yanke wa hukuncin an kama su ne da laifin "aikata kisa da kuma alaka da kungiyoyin ta'adda", in ji Dali.
Sai dai babu wani karin bayani game da sunayensu kuma mutum hudu ne daga cikinsu suka halarci zaman kotun, inda aka yanke wa sauran hukunci a bayan idonsu.
Kasar Tunisiya dai ta karfafa dokar hana aikata manyan laifuka tun shekarar 1991.
Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wasu hare-haren guda biyu na daban a 2015.