An kama akantan coci da satar ₦15m

Lokacin karatu: Minti 1

An yanke wa wani akantan coci hukuncin shekara 18 a gidan yari bisa laifin satar kudi naira milyan 15.5 na gidauniyar tallafi.

Ibrahim Aku na cocin Church of Brethren a jihar Adamawa, ya amsa laifi shidda da aka zarge shi da aikatawa da suka hada da kwace da kuma karbar kudi hanyar sojan-gona, a cewar wani rahoton jaridar Vanguard ta Najeriya.

Daga nan sai aka yanke masa hukuncin shekara uku kan kowane laifi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, wadda ta shigar da karar, ta wallafa hoton mai laifin, wanda wata babbar kotu ta yanke wa hukunci a arewa maso gabashin Najeriya.

Kotun ta saurari bayanan da ke cewa an bai wa akawun amanar adana kudin da cocin ke karba a matsayin na taimako.

Masu shigar da kara sun yi zargin cewa Aku, tare da wani mai taimaka masa wanda a yanzu ya shiga buya, sun yi takaddun banki na bogi amma ba su sa kudin a ma'ajiyar bankin cocin ba.

Rahotanni sun nuna cewa Aku ya tura wa mai taimaka masa naira 500,000 a matsayin ladansa.

Babbar kotun ta umarci Aku ya dawo wa cocin da kudinta kuma za a siyar da duk wani abu da ya siya da kudin.