An kashe sojoji 25 a Nijar

Rundunar soji a jamhuriyar Nijar ta ce wasu da ake zargin 'yan tada kayar baya ne sun kai hari wani sansanin soji, inda suka kashe kimanin sojoji 25 a kasar.

Harin na zuwa ne 'yan kwanaki gabanin gudanar da wani taro don duba ayyukan sojoji a yankin Sahel da za a yi a kasar Faransa da shugabannin kasashen Afirka ta yamma.

Harin ya faru ne kan wani sansanin soji da ke yammacin Nijar kusa da iyakar kasar da Mali.

Wajen yana da kusanci da inda aka kashe sojoji 71 wata daya da ya gabata a wani hari da kungiyar ISIS ta dauki nauyin kai wa.

Masu tada kayar baya da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda suna gudanar da ayyukansu a yankin yayin da Boko Haram kuma suka fi karfi a kan iyakar kasar da ke kudu maso gabas.

Rahotannin farko sun nuna cewa dakarun Faransa da takwaransu na Amurka sun kai dauki domin fatattakar masu tada kayar bayan.

Mali da Burkina Faso da kuma Nijar sun shafe tsawon shekaru suna yaki da masu tada kayar baya, sai dai adadin hare-haren da ake kai wa ya karu matuka duk da dubban dakarun da aka jibge domin yaki da matsalar taro.