Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Facebook zai hana saka bidiyon boge na 'deepfakes'
- Marubuci, Daga Sam Shead
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology reporter
Kamfanin Facebook ya bayar da sanarwar cire duk wani bidiyon da aka hada da manhajoji na musamman da ake kira "deepfakes" daga dandalinta.
Ana hada bidiyon "deepfakes" ne ta hanyar amfani da fasahar na'ura domin su zama kamar na gaske.
Kamfanin ya fadi hakan ne a wani shafiin intanet cewar irin wadannan bidiyon suna saba wa abin da abu na zahiri kuma babban kalubale ne ga masana'antar fasahar.
Duk da cewar bidiyon "deepfakes" ba su zama gama gari a shafin intanet ba, suna kara yaduwa.
Manhajojin na'ura mai basira na hada bidiyon mutane kamar na 'yan siyasa da kuma fitattun mutane ta hanyar hada wannan da wancan da maye gurbin wani abin ko kuma dauko wani abin na daban a sanya wa bidiyo ta yadda zai yi kama da na gaske
Facebook ya ce zai cire irin wadannan bidiyon idan har ya gano cewa an yi masu irin wannan hadin ta yadda mutum ba zai gane ba, ko kuma idan har bidiyon zai sa mutum ya yi tunanin wani ya furta wani abin da mutum bai ce ba.
"Akwai mutanen da aikinsu shi ne canja abin da kafar sadarwa ta ce kawai don su batar da mutane," in ji mataimakiyar shugaban hukumar tsarawa ta kamfanin facebook Monika Bickert.
Za a yi amfani da ma'aikatan kamfanin Facebook da kuma masu binciken gaskiyar lamari masu zaman kansu domin gano ko kuma tabbatar da sahihancin bidiyon.
Sabon tsarin ba zai shafi bidiyon da ake yi na kwaikwayon wani abu ba (parody) ko kuma na barkwanci (satire).
'Bangare mai wuyar sha'ani'
A watan Satumban da ya gabata ne kamfanin Facebook ya sanar da cewar zai bayar da gudummawar kudi dala miliyan 10 domin inganta fasahar gano hada bidiyon 'deepfake".
An hada bidiyon "deepfake" da Shugaban kamfanin Facebook kansa Mark Zuckerberg.
William Tunstall-Pedoe, wani masani a fannin kimiyyar komfuta wanda ya sayar da manhajarsa ga Amazon, ya fada wa BBC cewa kamfanin Facebook ya cancanci yabo kan kokarin magance abin da suka kira "bangare mai wuyar sha'ani".
Yace: "Maganar ko bidiyon ba na gaskiya ba ne ko kuma an yi shi ne domin batar da mutane daga gaskiya shi ne abin da ya da me ni. Ko da an yi amfani da shahararrun hanyoyin fasahar na'ura wato Artifcial Intelligence wajen yin su ko akasin haka, wannan ba shi da tasiri".
Sauran kamfanoni irinsu Google da Microsoft su ma suna ta kokarin magance matsalar deepfakes.
Kamfanin Facebook ya ce yana da niyyar aiki da cibiyoyin bayar da ilimi da gwamnatoci da kuma 'yan kasuwa wajen bankado mutanen da ke da hannu a deepfakes.
Kamfanin sada zumuntar da ke birnin California ya kara da cewa zai ci gaba da cire bidiyon da suka hadar da na nuna tsiraici da hotunan tashin hankula da kuma na batanci.
Bidiyon dan siyasan Amurka da aka gurbata
An yi ta sukar kamfanin facebook kan kin cire wani bidiyo na Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi, wanda ya samu karbuwa a bara. An hada bidiyon ne ta yadda zai yi kama da tana tauna kalamanta.
Sai dai Facebook ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba zai cire bidiyon ba karakashin sabon tsarin.
An ruwaito cewa kamfanin Facebook din ya ce, ba zai cire bidiyon Nancy Pelosi ba saboda bai cika sharuddan sabon tsarin ba da za su sa a cire shi.
"Bidiyon da aka hada da fasahar na'ura kawai za a cire: wadanda ke nuna mutane na fadin abin da ba shi ne na gaskiya ba."