Masu cin abinci a gidajen abinci na kokawa kan Butum-butumi

Kamfanin CES tech Expo dake Las Vegas ta kaddamar da wata butum butumin mage da zata dinga kai abinci ga abokan cinikayyarta.

Butum butumin mai suna BellaBot, wanda kamfanin fasaha ta PuduTech dake China ta kera na daya daga cikin jerin kirkire-kirkiren mutum mutumin da aka kaddamar dasu na wannan shekarar.

Akwai kuma wani butum butumi mai tafiya wanda UBTech Walker ta kera, wanda ke nuna ire-iren motsa jiki na yoga da za a iya yi .

Da kuma wani butum butumi na Charmin's RollBot, wanda ke hanzarin kai tolet paper ga bayukan dake bukatar hakan.

Daya daga cikin kwararrun yace, akwai yiwuwar kara samun ire-iren wadannan bajakolin butum butumi anan gaba.

BellaBot, wato butum butumin dake jiran abokan cinikayya akan tebur don basu abinci, butum butumin mage ce mai kima.

Wannan butum butumin na BellaBot da aka kera, ya kece na baya da aka taba yi mai bangarorin dake da amfani. BellaBot ya sha bam-bam da shi, inda yake dauke da wani abu mai nau'in talabijin dake nuna fuskokin butum butumin maguna.

Tana kukan mage a lokacin da ta iso teburan abokan cinikayya domin tunatar dasu, su dauki abincinsu.

Idan kuma masu cin abincin suka taba kunnen BellaBot, sai ya maida martani da nuna jin dadi.

Sai yace, hannunka akwai dumi, kamar yadda aka tsara shi ya fada.

Amma idan abokan cinikayyar suka ci gaba da taba shi har na tsawon wani lokaci, sai martanin ya canja.

"Yana yin fushi domin tunartawa da a daina kawo tsaiko cikin aikin shi, kamar yadda kamfanin ta bayyana.

A cewar kamfanin PuduTech, kamfanin Chinese din na kokarin cimma masu gidajen sayar da abinci a Chinan, wanda ke fama da matsalar daukan isassun ma'aikata.

An riga an fara amfanin da wannan butum butumin na wannan kamfanin a gidajen sayar da abinci 2000 a fadin duniya.

Kamfanin na shirin baje sababbin na'urarta a wani daki da aka kera wanda zaiyi kama da gidan sayar da abinci nan gaba, idan kamfanin CES ta bude a ranar Talata.

Sai dai zai yi wa butum butumi BellaBot wahala ya iya aiki yadda ya kamata a zahirance inji masanin fasaha, Paolo Pescatore na PP Foresight, saboda kalubalen da ake fuskanta na tafiyar da gidajen sayar da abinci a lokutan da aiki ke da yawa.

Ya kuma kara da cewa, ana tsammanin gidajen sayar da abinci zasu kara zama masu dogaro da na'ura mai kwakwalwa, in ba ta wannan hanyar ba, to ta wata hanyar.

Ana kuma bajakolin sabuwar butum butumi mai tafiya na kamfanin UBTech a CES na wannan shekarar.

A cewar makerinsa, butum butumin na abubuwa da dama na salon fada irin na Tai Chi da kuma motsa jiki na yoga, wanda yake nuna gagarumin ci gaba a harkar motsa jiki.

Yana nuna ci gaba da aka samu a harkokin motsa jiki irin ta yoga, kamar dai yadda ake tsammanin butum butumin da ke zaune a gidanka da iyalinka zai yi, yau bene ya sauko, yana dauke maka da kaya masu nauyi inji mai magana da yawun kamfanin, Jeff Gordon.

Wasu abubuwa da butum butumin ke iya yi kuma sun hadar da iya tura baro, da zanen hotuna da kuma zuba abin sha a kofi.

Sai kuma Kamfanin Procter da Gamble na Amurka masu kasuwancin "toli fefa" da ta jawo hankali zuwa ga fasahar da suka yi wanda ke cike gurbin bayuka da dakunan wanka: RollBot

"Kayi tunanin kai ne a wajen, kuma toli fefa ya kare, babu wanda ya ji kana kira." Mai gudanar da bincike na kamfanin P&G Gregg Weaker ya fadawa BBC.

Butum butumin zai gano inda kake a gidan ya kuma kai maka sabon toli fefar.

Ana kiran butum butumin RollBot ta Bluetooth a wayar hannu ta zamani.

Sai dai, P&G a yanzu bata shirya sanya wannan fasahar a kasuwa ba - inda hakan ke nufin za a jira zuwa wani lokaci na amfani da wannan fasahar.

Godiya ga ci gaba da aka samu a iyawar komfutoci da kuma manhajoji, butum butumi sannu a hankali zasu inganta a bayyana kawunansu da kuma kwaikwayon abubuwan da dan adam zai iya yi a hasashen Mista Pescatore.

Ya kuma bayyana cewa, a yanayi da ake na rigingegeniya a kasuwanni, butum butumi masu sa nishadi zasu fi cin kasuwa.

Ya kara da cewar, yana daya daga cikin fasahohin dake bunkasa.

A sa ran samun butum butumi masu sa nishadi a shekaru masu zuwa.