Fashewar gas ta kashe mutane 5 a Kaduna

Lokacin karatu: Minti 2

Hatsarin facewar tukunyar gas ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar tare da raunata wasu guda hudu a wani shagon sayar da gas da ke unguwar Sabon Tasha a garin Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Mazauna yankin sun kadu matuka sakamakon bindigar da gas din ya yi, wanda har ya shafi wasu shagunan da ke kusa da wanda lamarin ya faru.

Wasu hotunan da jama'a suka yi ta yadawa a shafukan intanet sun nuna irin barnar da lamarin ya yi.

A sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan da wadanda suka samu rauni, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya yaba wa 'yan kwana-kwana da sauran hukumomi bisa matakan gaggawa da suka dauka bayan aukuwar lamarin.

"Gwamnatin jihar Kaduna na mika ta'aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin gas a yau," in ji Aruwan. "Muna taya su alhinin wannan bala'i da ya faru."

Shi ma da yake mika ta'aziyyarsa, dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya Sanata Uba Sani, ya yi addu'ar samun rahama ga mamatan.

"Ina jinjina ga kokarin da 'yan kwana-kwana da sauran jami'an tsaro suka yi wurin shawo kan lamarin.

"Ina rokon Allah Ya yi wa mamatan rahama sannan Ya bai wa wadanda suka samu rauni sauki, wadanda suka yi asara kuma kada su yanke kauna."