Australia za ta tura soja 3,000 don kashe wutar daji

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da gobarar daji ke ci gaba da ruruwa a fadin Australia, firai minista Scott Morrison ya ce kasar za ta tura dakaru 3,000 domin taimakawa wajen kashe wutar.

Ministan tsaron kasar ya ce wannan shi ne karon farko da wutar dajin ta kai wani mataki da ba a taba gani ba.

Gomman mutane sun bace yayin da wutar ta cinye gidaje sama da 1,000 a kudu maso gabashin kasar a ranar Asabar.

Tuni aka bai wa mazauna umarnin ficewa daga wasu yankuna. Sararin samaniya ya yi jawur tare da iska mai cike da kurar toka a kudu maso gabashin Australia.

A yankuna masu tsaunuka kuma jami'ai sun shaida wa mazauna cewa sun makara wurin fita daga wuraren, don haka aka ba su shawarar zama a cikin gidajensu.

A yankuna uku ne wutar daji ta tashi a yankin Victoria, inda girman wutar ya kai hekta 6,000 a daren jiya.

Zuwa wayewar gari wasu karin wutar daji 73 sun tashi a yankin, 53 daga ciki na kan ci, 13 kuma aka ayyana cewa sun kai matataki mai hadari.

Fadin kasar da ta kai hekta 900,000 ne gobarar ta kona a Australia a cewar hukumomi.

Sai dai sun ce yawan mutanen da suka bace ya ragu daga 28 zuwa guda shida.

Yawan wuraren da wutar dajin ta tashi a fadin yankin New South Wales (NSW) ya kai 100 kuma fiye da rabinsu ba za a iya tunkarar su ba a cewar hukumar 'yan kwanakwanan yankin.

Shugban hukumar Shane Fitzsimmons ya bukaci mazauna da su takaita amfani da lantarki, yayin da rahotanni ke cewa layukan sadarwa sun daina aiki a yankin.

A tsibirin Kangaro kuma wutar ta lalata kashi daya bisa hudu na fadin kasar yankin ciki har da wani bangare na gandun namun daji na Flinders Chase National Park.

Wasu hotuna da aka wallafa sun nuna yadda wutar ta haifar da wani irin yanayi na iska da cida.

Abin da ake yi

Bayan tura sojoji mista Morrison ya ce gwamnatin kasar ta ware dala miliyan 20 domin karbar hayar manyan jiragen kashe gobara.

Ya ce ma'aikatar tsaron kasar za ta samar da matsuguni ga mutane.

A ranar Juma'a sojin ruwan kasar sun kwashe masu yawon bude ido da mazauna 1,000 da suka makale sakamakon wutar daji a garin Mallacoota da ke gabar Victoria.

Wadanda aka fara kwashewa sun isa zirin Mornington a ranar Asabar.

Jirgin HMAS Adelaide, zai bar Sydney a ranar Asabar, inda zai yi zaman jiran ko-ta-kwana domin kwashe mutane.

NSW ta ayyana dokar ta-baci ta mako guda tare da bukatar masu yawon bude ido da su kaurace wa wasu yankunan da ke bakin gaba.

'Yan kwanakwana 3,000 ne ke aiki a NSW, a cewar News.com.au.

Me ya faru?

A watan Satumban 2019 ne wutar dajin ta fara tashi a Australia.

Baya ga sanadiyyar mace-mace, gobarar dajin ta cinye gidaje sama da 1,300 da miliyoyin eka na gandun daji.

Masu hasashen yanayi sun danganta tashin wutar dajin da matsanancin zafi sakamakon sauyin yanayi a tekun Indiya.

Yawancin yankunan Australia na fama da karancin ruwan sama, abin da ke sa wutar kara yaduwa cikin sauki.

Firai minista Scott Morrison ya sha suka game da yadda ya tunkari matsalar, musamman saboda tafiyar da ya yi lokacin hutunsa zuwa Hawaii, da kuma rashin daukar batun sauyin yanayi da muhimmanci.

Amma a taron manema labarai da ya yi ranar Juma'a, mista Morrison ya ce ya fahimci irin wahalar da mutane suka sha da irin yadda suke ji.