Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An zana kalaman kyamar Musulunci a jikin masallaci a London
An zana taken da ke nuna kyama ga Musulunci a jikin wani gini da ke kusa da wani masallaci a Kudancin London.
An gano alamar jikin wani gini a kusa da cibiyar addini da ke kan titin Brixton da karfe 11:00 agogon GMT.
'Yan sandan yankin sun ce suna aiki da karamar hukumar Lambeth domin cire ''kalaman batancin'' daga jikin ginin ba tare da bata lokaci ba.
Hukumar 'yan sandan ta kara da cewa ta na gudanar da bincike don gano wanda yake da hannu a lamarin.
Sadiq Khan ya ce bai ji dadin ganin rubutun ba wanda aka lika a ginin 'yan kwanaki bayan wasu kalaman batanci ga Yahudawa da aka manna a shaguna da wurin ibadar yahudawa a arewacin London.
Magajin garin London ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ''duk kalaman nuna wariya alama ce ta tsoro kuma masu laifi za su fuskanci doka.''