Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jam'iyyar APC ta 'dare' gida biyu
A Najeriya, rikicin cikin gida na ci gaba da ruruwa a jam'iyyar APC mai mulkin kasar, har wasu jiga-jigan jam'iyyar na ganin kamata ya yi shugaban jam'iyyar na kasa, Adam Oshiomhole ya sauka daga mukaminsa, don samun zaman lafiya.
Rikicin da ake ganin tamkar 'yan jam'iyyar adawa ne ke yada jijta-jita akai, yanzu ya fara bayyana a fili karara, inda rashin jituwa tsakanin shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomole da wasu 'yan jam'iyyar a jihohi.
Da dama daga 'yan jam'iyyar na ganin hanya daya da za a iya dinke wannan baraka ita ce shugaban na jam'iyyar ta APC ya sauka daga mukaminsa.
Mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa a arewacin Najeriya Sanata Lawal Shu'aibu, ya ce "ciyamomin jiha na jam'iyyarmu sun ce su ba su yarda ba sai Oshiomole ya tafi."
Ya kara da cewa "babu yadda za a yi jam'iyya ta ci gaba a haka saboda irin rabuwar kan da ke jam'iyyar ba abu ne da za a iya dinkewa cikin sauki.
Tana dinkuwa amma sai dai da za a samu ya ce (Oshiomole) ya sauka to da duk mai korafi zai daina."
To sai dai kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar na kasa a jam'iyyar sun ce batun kiraye-kirayen da ake yi wa Oshiomole ya sauka daga kan mukami ba dai-dai ba ne.
Ibrahim Masari ya ce "ko miskala zarratun shugaban jam'iyyar APC ba zai sauka ba, idan an kama shi da wani laifi ne to abin da za a yi shi ne kiran babban taron jam'iyya.
Sai a zayyana duk laifukan da ake tuhumar sa da su a gaban wannan taro sannan sai a ce an sauke shi daga mukami idan an same shi da laifi.
Amma ba wai kawai rankadama wani mutum ya zo ya ce wai shugaban jam'iyya ya sauka ba."
Sharhi, Tukur Abdulkadir
Dr Tukur Abdulkadir na jami'ar jihar Kaduna wanda masanin siyasar Najeriya ne ya ce dole ne shugabannin jam'iyyar su tsaya su kalli al'amarin su gyara.
Ya ce idan har 'yan jam'iyyar ba su farka ba to jam'iyyar mai mulki na daf da rugujewa kuma bai zama lallai ta yi tasiri ba a zabe mai zuwa na 2023.
Sai dai Ibrahim Masari na jam'iyyar ta APC ya yi inkarin hasashen rushewar jam'iyyar, inda ya ce rikicin da jam'iyyar ke ciki na nuna irin tumbatsar da ta yi ne.
"Ai kananan jam'iyyu ba sa samun rikicin gida, batun cewa jam'iyyar APC na dab da rushewa abin da dariya ne...hahahahahahah...."
Abin jira a gani dai shi ne ko shugaba Muhammaud Buhari zai sa baki wajen ganin rikicin bai kai mizanin ruguza jam'iyyar ba.
A baya dai shugaban ya sha cewa ba zai shiga lamarin da ba huruminsa ba, kafin daga bisani a 'tilasta' shi saka bakin mafi yawanci a lokacin da bakin alkalami ya riga ya bushe.