Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Suu Kyi ta yi watsi da zargin kisan kiyashi a Kotu
Jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta kare kasarta daga zargin aikata laifukan kisan kiyashi a gaban kotu.
Aung San Suu Kyi, wadda ta karbi lambar Nobel ta zaman lafiya, ta mayar da martani a kan zargin da ake cewa an aikata kisan kiyashi a akan Musulmi, 'yan kabilar Rohingya a kasarta.
A farkon jawabinta, Suu Kyi ta kira karar da aka shigar a kan Myanmar a matsayin marar tushe.
Ta ce tashe-tashen hankulan da aka samu a Rakhine, inda yawanci a nan ne 'yan kabilar Rohingya suke, abu ne da ya samo asali tun a baya.
Dubban Rohinjawa aka kashe, yayin da wasu fiye da dubu 700 kuma suka tsere zuwa Bangladesh da ke makwabtaka da Myanmar a 2017, lokacin da sojoji suka murkushe 'yan addinin Bhudda.
A kodayaushe dai, Myanmar kan hakikance cewa, tana kokarin dakile barazanar da take fuskanta ne daga masu tsattsauran ra'ayi a jhar Rakhine, lamarin da ita kanta Ms Suu Kyi kan bayyana da cewa shi ne ya rura wutar rikicin tsakanin 'yan sa kan Rohingya da dakarun gwamnati.
Da take bayani a kan ko dakarun kasarta sun yi amfani da karfin tuwo a wasu lokutan, Ms Suu Kyi, ta ce duk sojan da aka samu da aikata laifin yaki, to za a hukunta shi hukuncin da ya dace da shi.
'Muna goyon bayanta, kana mun yarda da ita. Ita ce kadai wadda za ta kawo zaman lafiya a kasarmu tare da kawo karshen mummunan yanayin da ake ciki a kasarmu'.
Me ya sa aka kai Myanmar kotu?
Kasar Gambia, wadda karamar ce ta Muslmai a yammacin Afirka, ta shigar da kara a gaban kotun a madadin sauran Musulmai na kasashen duniya.
Abin da Gambia ta bukata shi ne, a shaida wa Myanmar cewa ta dai na kisan babu gaira ba dalili da ake yi a Myanmar.
Gambia ta dauki matakin ne bayan ministan shari'ar kasar ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijrar Rohingya a Bangladesh inda ya ji irin yadda aka ci zarafinsu.
Wadanne zargi ake yi wa Myanmar?
A farkon shekarar 2017, akwai 'yan kabilar Rohingya da dama a Myanmar, yawancinsu kuma suna zaune ne a jihar Rakhine.
Amma Myanmar da yake 'yan addinin Buddha sun mamaye ta, sai suke daukar su a matsayin bakin haure don haka suka ki ba su damar zama 'yan kasa.
Daga nan sai 'yan kabilar Rohingya suka fara korafin ana takura musu, inda a shekarar ne dai sojojin kasar suka fara afkawa jihar Rakhine.
Tun daga nan ne rikici ya fara.