Jirgin saman dauke da fasinjoji ya yi batan dabo

Jirgin sojin saman Chile ya shirya domin tashi daga filin jirgin saman Santiago a watan Maris din 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin saman kasar Chile suke aiki da jirgin samfurin C-130
Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar sojin saman kasar Chile, ta ce wani jirginta dauke da fasinja 38, ya yi batan dabo a kan hanyarsa ta zuwa Antarctica.

Jirgin samfurin C-130, ya tashi ne daga Punta Arenas da misalin karfe 5 saura minti 5 agogon kasar.

Daga cikin wadanda ke ciki jirgin akwai ma'aikatan jirgin 17 da kuma fasinja 21.

Mutanen cikin jirgin dai sun yi wannan tafiya ne domin kai kayan aiki ga sojojin da ke wani sansani a tsibirin King George da ke Antarctica.

Me ya faru?

Shugaban rundunar sojin sama ta kasar, Janar Eduardo Mosqueira, ya sheda wa kafafen yada labarai na kasar cewa, jirgin bai bayar da wata alamar neman dauki ba.

Ya ce, jirgin wanda wani kwararren matukin jirgi ke tukawa, ya yi saukar gaggawa ne inda ya taba ruwa bayan man sa ya kare.

Tuni dai aka tura masu aikin ceto domin neman jirgin tare da ceton wadanda ke cikinsa.

Wata sanarwa da rundunar sojin saman kasar ta Chile ta fitar ta ce, sai da jirgin ya kusa kaiwa inda zai je, domin ya ci fiye da rabin tafiyar da zai yi, sannan aka daina magana da ma'aikatan jirgin.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ruwan Drake Passage, wani bangare na kogin da ya hade da tekun South Atlantic da na South Pacific, wadanda aka san su da rashin kyakkyawan yanayi.

To amma, rundunar sojin sama ta Chile ta ce, yanayin da ake ciki a lokacin da jirgin ya bata yana da kyau, haka kuma akwai wadataccen man da kai su inda za suje.

Su waye a cikin jirgin?

Fasinjoji uku daga cikin wadanda ke cikin jirgin sojojin Chile ne, sai kuma injiniyoyi biyu fararen hula wadanda aka dauka domin su je su yi wani dan aiki a sansanin sojin da za su je. Daya kuma dalibi ne a jami'ar Magellanes, sai kuma sauran fasinjoji 15 wadanda ma'aikata ne a rundunar sojin saman Chile.

Kazalika jirgin na dauke da ma'aikata 17, wadanda ba'a kai ga bayyana sunayensu ba.

Tuni rundunar sojin ta ce ana fara tuntubar iyalan wadanda ke cikin jirgin.

Haka kuma an tura jiragen sama guda takwas da na ruwa guda hudu domin aikin neman jirgin.

Shugaban kasar ta Chile Sebastián Piñera, ya bayyana a cikin shafinsa na twitter cewa, ya kadu matuka da samun labarin, sannan kuma tuni ya garzaya zuwa wajen da ake aikin neman inda jirgin ya shiga.