Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka yi bikin yaye 'yan Boko Haram da suka tuba a Nijar
An yi bikin yaye kashin farko da tsoffin 'yan Boko Haram da suka tuba kuma aka ba su horon gyara halayya Jamhuriyyar Nijar.
An gudanar da bikin 'yaye tsoffin 'yan kungiyar Boko Haram din ne a cibiyar gyara masu rayuwa da ke garin Goudoumaria a jihar Diffa mai makwabtaka da jihar Borno ta Najeriya.
Tubabbun da aka yaye kuma aka gyara halayyarsu sanye da farin tufafi sun yi rantsuwar yi wa kasa biyya da ci gaba da zaman lafiya.
Daya daga daga cikinsu, ya ce sun tuba kuma sun yi alkawalin ba za su sake taimakawa ayyukan Boko Haram ba.
Ministan harkokin cikin gida na Nijar, Bazoum Mohamed ya shaida wa BBC cewa an koya wa tubabbun addini na gaskiya da sana'o'in hannu bayan da suka tabbatar da sun tuba sun kuma daina aikata ta'addanci.
Ya kuma yi kira ga jama'a da su sani cewa yanzu wadannnan ba 'yan Boko Haram ba ne, musulmi ne, yara ne za su koma gidajensu domin su yi rayuwa kamar kowa.
"Muna so a karbe su da hannu biyu a matsayin yara da suka dawo gida, bayan da suka yi batan kai sun gyaru, gwamnati ta gyara su, sun shiga hanyar addinin musulunci" In ji Bazoum.
An yaye tsoffin 'yan Boko Haram din sama da 100 ne wanda hukumomin kasar Nijar suka shirya bisa tallafin Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomin kasashen duniya.
Wannan dai wani bangare ne na kawo karshen rikicin ta'addanci da aka shafe tsawon shekara goma ana yi.
Bikin yaye tubabbun 'yan Boko Haram din dai ya samu halartar jami'an gwamnati da na Majalisar Dinkin Duniya da wakilan diflomasiyar daga tarayyar Turai da kuma Amurka.
Tsaffin 'yan Boko Haram din da a yanzu za a sake su, su ne kashin farko na daruruwan 'yan Boko Haram da suka mika wuya ga hukumomi domin a yi musu afuwa.
Sun shafe shekara uku a cibiyar da ke yankin Goudoumari a jihar Diffa inda aka yi musu gyaran hali tare da cire musu akidar ta'addanci.
Yayin da suke shirin shiga al'umma, ana ganin za su fuskanci babban kalubale na ci gaba da kyamatarsu da kuma rashin yarda da su daga al'umma.
A lokacin da suke cikin kungiyar ta Boko Haram dai, sun taka rawa wajen kai hare-haren kungiyar.
Wasu a cikinsu sun ce tilasta su aka yi shiga kungiyar ta Boko Haram bayan far wa kauyukansu yayin da sauran kuma suka ce wanke musu tunani aka yi.