Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sudan ta soke dokar kayyade dabi’un mata da sutura
Sudan ta soke wata doka mai tsauri wadda ta kayyade dabi'un mata da irin suturun da ya kamata su saka a bainar jama'a.
A shafin Twitter, Firai Minista Abdalla Hamdok ya yi jaje ga matan da suka jure wa irin wannan ''wulakanci'' da ya yi sanadiyar kafa wannan doka.
Gwamnatin rikon kwaryar kasar ta kuma rushe tsohuwar jam'iyyar Shugaba Omar al-Bashir.
Mista Bashir ya karbi mulki ne a wani juyin mulki a 1989 kuma ya mulki kasar kusan shekaru 30.
An hambare Shugaban ne bayan wata zanga-zanga da aka shafe kwanaki ana yi a watan Afrilu.
A yanzu haka gwamnatin hadin gwiwa tsakanin sojoji da farar hula ke mulkar kasar inda Shugaba Hamdok ne firai minista.
Me dokar ke cewa?
A wani rahoto da wasu kungiyoyin bayar da agaji suka fitar a 2017, sun bayyana dokar kayyade dabi'un mata a matsayin abin da ya saba wa hakkin dan adam.
Sun bayyana cewa dokar an yi ta ne domin ''hana mata rawar gaban hantsi da jin dadin rayuwa.''
Dokar dai na sa ido da kuma lura da wadanne irin kaya mata ke sakawa, da wadanda suke magana da su da kuma irin ayyukan da za su yi, inda duk wadda ta saba wa dokar ke fuskantar hukuncin bulala, a wani lokacin kuma jifa ko kuma kisa.
Rahoton ya bayyana cewa dokar ta zama wata hanya da ''jami'an tsaro ke amfani da ita wajen cin mutunci.''
Wata mai kare hakkin bil adama, Hala al-Karib ta shaida wa BBC cewa soke dokar wani babban mataki ne na ci gaba ga kasarta, inda ta bayyana cewa majalisar kasar ta aiwatar da manufofin tsohuwar gwamnatin kasar ne ''wadanda suke da alaka da ta'addanci da kuma nuna wariya.''