Matar da ta tsira bayan gingimari ta latse motarta

Wata mace mai shekara 27 ta ji mummunan rauni sakamakon danne motarta da babbar mota ta yi a kudancin birnin Port Elizabeth mai cike da bakar fata 'yan Afirka.

'Yan sanda sun ce direban a gingimarin ya tsaya a gefen hanya tare da shiga makarantar firamare ta Parsons Hill don daukar 'ya'yansa.

Motar ta gangaro daga tudu, tare da murkushe motar da matar ke ciki.

Motar ta tamutse a kan kwalta, inda matar da ake ciki ta kwashe tsawon minti 40 kafin jami'an sun zakulo ta.

Matar dai ta tsira da rai, amma an garzaya da ita asibiti sakamakon munanan raunin da ta ji da suka hada da karaya.