'Ina hana cikina abinci na sayi data da kudin'

    • Marubuci, Daga Gaius Kowene
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kinshasa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bonheur Malenga, dalibin wata jami'a ne a kasar Congo, ya samu kansa cikin tsaka mai wuya, kan ko dai ya hana cikinsa abinci ya sayi data don hawa intanet.

''A lokacin ina jin matsananciyar yunwa, na kasa tantance shin datar intanet ta sa'a 24 ya kamata in saya ko kuwa abinci?'', in ji dalibin yayin wata hira da BBC.

Dalibin mai shekara 27, yana karatun injiniya ne kuma iyayensa ke tallafa masa, to amma yana kashe kudin da ya wuce kima saboda amfanin da yake da internet don binciken bangaren da yake karatu na lakume masa kudi.

Malenga dai na zaune a birnin Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, kasar da ma'aikata ke kashe kashi 26 cikin albashinsu ko kudin da suke samu ga intanet ta wayar salula wadda ita ce sassaukar hanyar amfani da yanar gizo.

Ya kara da cewa "Na cewa kaina yunwa ba za ta kashe ni ba idan ban ci abinci na kwana daya da yini ba. Don haka kawai sai na rufe ido na sayi data na zauna da yunwa.''

Malenga ya ce, yawancin abokansa na kwana da yunwa saboda su hau intanet.

Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo na daga cikin kasashen duniya da intanet ke da matukar tsada, kamar yadda rahoton gamayyar kungiyoyin da ke rajin saukaka kudin intanet ta fitar a shekarar nan.

Kungiyoyin na kokarin ganin an samar da sassaukar data idan mutum ya biya kashi 2 cikin 100 na albashinsa a wata inda zai samu data mai karfin 1GB.

'Mai shagon intanet ya kwace min takalmi'

A wani bangare na kasar, nisan kilomita 2,000 daga birnin Kinshasa, wani matashi Eric Kasinga ya tuna abin da ya same shi shekaru kadan da suka gabata.

Kamar sauran matasan da ke garin Bukavu, Eric na zuwa shagon intanet don shiga yanar gizo. A lokacin yana son cike takardun neman gurbin karatu a Jami'ar Netherlands.

"Intanet din na tafiyar hawainiya, don haka na yi sa'a uku ina cike abubuwan da suka kamata maimakon sa'a daya.''

Ya ce kudin da ke hannunsa na yin sa'a daya ne kacal a shagon intanet din.

Ya bayyana abin da manajan shagon ya yi masa, a tunaninsa wannan zai sa ya kawo kudin da ake bin shi.

Manajan ya fara yi masa fada da daga murya tare da cewa ''intanet ba ta talakawa ba ce.''

Kan kudin nan manajan ya cire wa Eric sabon takalmin da ke kafarsa, dole ya daba sayyadarsa tun daga shagon har zuwa gida.

''Kunya ta kama ni na rasa yadda zan yi,'' in ji Eric.

Matashin da ya kammala karatu yake kuma aiki a wata kungiya da ke tattauna batutuwan da suka shafi jama'a, ya ce bai samu karasa cike takardun neman gurbin karatun da ya fara.

Bayan mako guda ya koma shagon intanet din don karbo takalminsa, amma tuni manajan ya sayar da su.

"Bai kamata wani ya samu kansa a wannan hali ba saboda intanet,'' in ji Eric.

Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo ita ce kasa ta hudu mai yawan al'umma a Afirka, kashi biyu cikin uku kenan na al'ummar Yammacin Turai, kuma kasa ce mai albarkar ma'adinai da ake amfani da su don hada wayar salula.

Amma duk da hakan yawancin 'yan kasar suna shan wahala, ba sa samun tsaftataccen ruwan sha, da wutar lantarki, da uwa-uba kiwon lafiya.

A wajen su samun damar intanet da MDD ta sanya a matsayin 'yancin dan adam a shekarar 2016, wata aljannar duniya ce.

Babban kamfanin sadarwa na Congo ya yi kiyasin cewa kashi 17 cikin 100 na 'yan kasar duk na samun intanet.

Wani rahoton na baya-bayan nan ya nuna yadda ake samun karuwar rata tsakanin masu amfani da intanet a Afirka.

Sama da kashi 33 cikin 100 na maza ne ke samun intanet, yayin da mata suka dauki kashi 22.6.

Kodjo Ndukuma, kwararren mai rajin kare hakki ne ta internet, da ke aiki a Jami'ar Université Pédagogique Nationale (UPN) a Kinshasa, ya ce akwai kwararan dalilai uku da ke sanya tsadar intanet a Congo.

1. Ba wanda ya san ainahin nawa ne kudin intanet

"Kana sanin abin da kamfanin sadarwar ke cajinka kudin data idan ka yi la'akari da kudaden da ake dora musu na haraji, da yawan mutanen da ke amfani da layinsu.''

Wadannan kudade ne na aika sakon murya, amma babu kamfanin da ke magana akan kiran da aka yi ta intanet, ma'ana bai kamata kamfanonin su cike gibin nan kan kudin da abokan hulda ke amfani da layukansu ba.

Farfesa Kodjo ya ce babbar matsalar ita ce ba a bai wa kamfanonin sadarwa 'yancin kansu don sanya kudi kan abubuwan da ya shafi hulda da masu amfani da layukansu.

2. Rashin samun kishiyoyi a fagen sadarwa

Shekaru da dama rashin yawan masu amfani da layukan sadarwa na daga cikin abin da ya janyo tsadar.

Abinda kamfanonin nan za su yi bai wuce su amince da yin abu kuma babu wanda ya isa hana su.

Ya bayar da misali da watan Afrilun 2016, lokacin da kamfanonin sadarwar kasar suka fitar da sanarwar amincewa da kara kudin data na kashi 500.

3. Matsanancin haraji

"Kamfanonin sadarwa na biyan makudan kudaden haraji, tun daga matakin gwamnatin tarayya har zuwa kananan hukumomi,'' in ji farfesan.

"Su kuma sai su huce akan abokan huldarsu."

Gwamnatin Congo dai na fuskantar matsin lamba, da kiran ta shiga lamarin bayan wata zanga-zanga da matasan wata kungiya mai suna La Lucha suka yi.

Kungiyar ta mayar da kanta ta kare hakkin masu amfani da intanet tsakanin watan Mayu zuwa Oktoba, sun gudanar da zanga-zanga 11 a cikin kasar da kiraye-kirayen a rage kudin data.

"Hukumar da ke sa ido kan kamfanonin sadarwa sun shaida mana cewa akwai daidai ka'idar da za su iya shiga lamarin kan yadda kamfanonin sadarwa ke gudanar da ayyukansu da hulda da abokan kasuwanci,'' in ji daya daga cikin 'ya'yan kungiyar La Lucha, wato Bienvenu Matumo.

"Amma duk da haka, muna son gwamnati ta dauki mataki maimakon zura ido ana cutarmu."

Shi ma ministan fasaha da sadarwa na Congo ya bukaci kamfanonin sadarwa da kungiyar La Lucha su zauna don tattauna yadda za a magance matsalar saboda ita kanta gwamnati ba ta da hurumin tsunduma kai tsaye kan batun kamar yadda kundin tsarin mulki ya haramta mata.

Amma zaman tattaunawar farko ya fuskanci cikas, ba a samar da wata kwakkwarar magana ba, kuma internet na ci gaba da tsada da rashin karfi.

'Tsoron kashe kudi'

Mata 'yan kasuwa kamar Vanessa Baya ta san ba lallai a samu dacewa nan kusa ba idan dai ana batun tsadar intanet.

Kasuwancinta ya dogara ga intanet, "Babbar matsalar ita ce ba mu da tabbas kan internet kafin a yi batun tsadarta. Ina amfani da kamfanonin sadarwa daban-daban don samun mai karfi a ciki,'' in ji Baya.