Najeriya: Hana sayar da mai a kusa da iyakoki ya jefa jama'a cikin kunci

Al'ummomi a wasu yankunan da ke iyakokin Najeriya da wasu makwabtanta sun ce suna ji a jika sakamakon hana kai man fetur da Hukmuar Kwastam ta kasar ta yi.

A makon jiya ne dai Hukumar ta haramta kai man fetur da dangoginsa yankunan da ba su fi kilomita 20 ba daga iyakokin kasar.

A Baburan jihar Jigawa dake arewacin kasar alal misali, al'ummar yankin sun shaida wa BBC cewa matakin na baya-bayannan ya haddasa rufe gidajen man fetur da dama.

"Ba mu san inda za mu je mu shawo man ba ma ballantana mu san nawa za mu dinga daukar fasinja", inji wani mai sana'ar acaba a yankin.

A cewarsu, a wasu gidajen man ana samun layuka wajen sayen man a kan farashi mai tsada, abin da ya bude kasuwar 'yan bumburutu.

Sun kara da cewa jami'an hukumar ta kwastam suna samame kan duk wani gidan mai da aka samu yana sayarwa.

A Sokoto ma

A Ilela na jihar Sokoto ma, jama'a sun ce kashi 90 cikin 100 na gidajen man dake yankin na rufe.

Man da ake sayarwa a kan N145 da gwamnati ta kayyade, a cewarsu, yanzu farashinsa ya ninka sau kusan uku.

Ita dai gwamnatin Najeriya ta ce ta dauki matakin ne domin magance matsalar shigo da albarkatun mai ta barauniyar hanya da kuma hada baki da masu gidajen man wajen fitar da man zuwa wasu kasashen inda ake sayar da shi da tsada.

Sai dai an samu bambanci a wasu yankunan dake kusa da iyakokin kasar inda a garin Gurum da ke jihar Adamawa, wani mazaunin yankin ya ce gidajen mai na gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

A cewarshi, matakin gwamnatin bai kai wajensu ba tun da gidajen man suna cin kasuwarsu kamar yadda suka saba sai dai kuma ana sayar da fetur din ne a kan N150 duk lita sabanin farashin gwamnati.

A baya bayannan ma, kungiyar masu kamfanonin sadarwa a Najeriya, ALTON ta koka game da matakin na gwamnatin Najeriya wanda ta ce ya shafi na'urorinta dake yankunan da abin ya shafa saboda hukumomi sun hana kai musu man dizel.

Sai dai tuni majalisar wakilan kasar ta sa baki inda ta bukaci hukumar ta Kwastam ta janye hanin na sayar da man fetur da sauran dangoginsa a gidajen man da ke yankunan kan iyakar.

Wani kudiri da Honourable Sada Soli Jibiya ya gabatar a gaban Majalisar Wakilai ya nemi a janye takunkumin saboda mawuyacin halin da al'ummar yankunan ke ciki.

A cewar dan majalisar, ''Akalla akwai garuruwa guda 2,000 a kananan hukumomi 105 a cikin jihohi 21 da suke kan bodar Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Benin.''

Ya kuma ce yawan mutanen da ke zaune a yankunan ya kai miliyan 50 kuma "abin nan arziki ne na kasa kuma abin da yake tafiyar da al'amuransu na yau da kullum an ce kar a kai musu.''

Ya bayyana cewa kamata ya yi kwamitocin majalisa dake kula da shige da fice da wanda ke kula da aikin kwastam da kuma wanda ke kula da man fetur su zauna da shugaban hukumar da sauran masu ruwa da tsaki a kan hada-hadar man fetur a kasa domin samar da maslaha tun kafin mutane su shiga halin da zia kawo rauni akansu.

A ranar 6 ga watan Nuwamba ne dai hukumar ta kwastam ta fitar da sanarwar sanya takunkumin a dukkanin yankunan dake kusa da iyakokin Najeriya.