Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Maulud: Kacici-kacici kan rayuwar Annabi Muhammad SAW
An fara wallafa wannan kacici-kacici ne a shekarar 2019 da ta gabata, wato 1441 bayan hijira kenan, sai muka sake wallafa ta a yau.
Galibin Musulmi sun yi amanna cewa ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal aka haifi Annabi Muhammadu SAW - akwai sabanin malamai game da wannan batu.
Saboda rinjayen wadanda suka yarda da ingancin wannan kauli ne muke gabatar maku da wannan kacici-kacici domin auna saninku game da rayuwarsa.
Sai ku shiga ciki domin gwada hazakarku.
Mun bai wa malamai sun duba amsoshin domin tabbatar da sahihancinsu.