Sojojin Najeriya sun nesanta kansu daga bidiyon cin zarafi

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojan Najeriya ta nesanta kanta daga wani bidiyo da ya bulla a intanet, wanda ke nuna wasu sojoji suna azabtarwa tare da kisan wani da ake zargin dan Boko Haram ne.
A wata sanarwa da ta aike wa manema labarai, rundunar ta ce ka'idojin aiki sun haramta wa dakarunta cin zarafin mutane, a saboda haka aikin nasu "abin Allah-wadai ne".
A karshen makon da ya gabata ne dai aka ga wasu sojoji a bidiyon suna harbe wani da aka ce dan Boko Haram ne bayan sun ja shi a kasa hannayensa daure da igiya sannan suka cilla shi cikin rami kuma suka harbe shi.
Ana iya jin wanda ya dauki bidiyon yana cewa: "Ku azabtar da shi, ku kashe shi domin ya ji radadi shi ma. Saboda irinku muka baro garuruwanmu muka zo Maiduguri. Maiduguri garina ne?"
Rundunar ta ce tuni ta kaddamar da bincike game da bidiyon da nufin gano wadanda suka aikata sannan kuma za a sanar da jama'a sakamakon binciken.
"An gargadi dakaru game da cin zarafin wadanda ake zargi duk kuwa da irin yadda ake bukatar samun bayanai daga gare su ko kuma girman abin da suka aikata.
"Duk sanda aka samu rahoto na irin wannan aikin za a dauki matakin ladaftarwa kan wadanda suka aikata da zarar an tabbatar."
Zargin cin zarafin masu laifi ko kuma wadanda ake zargi da laifin ba sabon abu ba ne game da sojojin Najeriya.
A shekarun baya gwamnatin Amurka ta ce ta yanke shawarar daina sayar wa da Najeriya makamai saboda cin zararfin bil'adama da sojoji ke yi a wuraren da suke aiki.
Ita ma kungiyar Amnesty Intaernational mai kare hakki ta sha yin irin wannan zargi, wanda gwamnatin Najeriya ta sha musantawa.











