Abubuwan da suka faru a Najeriya a wannan makon

    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

Wannan shafin na dauke da kadan daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya da kuma wasu abubuwan da suka shafi kasar da suka afku a wasu kasashen tun daga ranar 27 ga watan Oktoba zuwa 3 ga watan Nuwamba.

Kotun koli ta kori karar Atiku

BBC

A wannan makon ne kotun koli ta Najeriya ta kori karar da jam'iyyar PDP da dan takarar shugabancin kasar jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar suka shigar gabanta suna kalubalantar nasarar da hukumar INEC ta bai wa Shugaba Buhari a zaben 2019.

Alkalan kotun dai sun yi watsi da karar ne bisa rashin dacewarta a ranar Laraba.

A ranar 11 ga watan Satumba ne dai kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da karar da jam'iyyar ta PDP ta shigar ta neman a soke zaben na watan Fabrairu.

Kotun sauraron kararrakin zaben dai ta ce ta yi watsi da karar jam'iyyar PDP ne bisa gaza gamsar da kotun kan korafe-korafensu da suka hada da tafka magudi a zaben shugaban kasa da kuma ikirarin cewa Shugaba Buhari bai cancanci tsayawa takarar ba bisa rashin mallakar shedar kammala sakandare.

'Yan sanda sun kama Fasto mai gidan mari a Najeriya

BBC

A cikin wannan makon ne 'yan sanda a jihar Legas suka ceto mutum 15 da suka kasance cikin mari da sarka a wani gidan mari da wani fasto da ke ikirarin annabta yake gudanarwa a unguwar Ijegun a birnin.

An dai samu nasarar ceto mutanen ne tare da cafke faston bayan da 'yan sanda suka kai wani samame ranar Laraba sakamakon samun labari da suka yi.

Mutanen 15 wadanda suka hada mata da maza masu shekaru 15 zuwa 19, sun shaida wa hukumomi cewa sun shafe shekaru fiye da biyar a kulle a gidan faston.

Mahaifan matasan ne dai suka kai su gidan fasto domin nema musu maganin matsalar tabin hankali da sauran nau'in cututtuka.

'Hukuncin kisa ga duk wanda ya saci yaro'

BBC

A ranar Alhamis ne Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya bai wa ma'aikatar shari'a umarni da ta yi wa dokokin jihar kwaskwarima domin zartar da hukuncin kisa ga masu satar jama'a.

Gwamna Ganduje ya ce wannan ce kawai wata hanya da za a iya magance yawaitar salwantar mutanen musamman kananan yara da a baya-bayan nan ake sacewa a fadin jihar ta Kano.

A yanzu dai hukuncin masu satar jama'a a jihar shi ne daurin rai da rai.

Gwamnatin Bauchi ta gano ma'aikatan 'bogi' 41,000

BBC

A wannan makon ne gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta gano sunayen wadannan mutanen ne a cikin kundin bayanan masu karbar albashi da fansho duk da cewa ba su da lambar Tantance Asusun Banki ta BVN don haka ake da shakku kan sahihancin kasancewarsu ma'aikata ko 'yan fansho.

To sai dai wasu daga cikin ma'aikatan na cewa suna da wannan lamba, kuma su ma'aikata ne na gaskiya. Daya daga cikinsu da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa su na cikin mawuyacin hali.

''Yace kashi 70% cikinmu ga albashi muka dogara daman da albashin ake hidimadar iyalai, ga bashin da ma'aikata suka ci. Ina da mata uku da 'ya'ya 13, kudin da zan biya na makarantar yara ma ba a samu ba.

Kakakin Gwammnan jihar ta Bauchi Alhaji Mukhtar Muhammad Gidado ya shaida wa BBC cewa da zarar gwamnatin jihar ta kammala bincike za a biya wadanda aka tabbatar da sahihancin kasancewarsu ma'aikata ko 'yan fansho.

Buhari ya halarci taron kasuwanci a Saudiyya

FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara Riyadh babban birnin Saudiyya inda ya halarci taron zuba jari karo na uku da kasar ta Saudiyya ta jagoranta.

Taron na yini uku mai taken "Me nene mataki na gaba ga kasuwancin duniya," ya mayar da hankali ne kan yadda za a inganta fasaha domin amfanin duniya a nan gaba.

Bayan taron, Shugaba Buhari ya je birnin Makkah tare da wasu masu bashi shawara domin gudanar da Umrah.

Ruwa ya hallaka mutum biyar a Kaduna

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Cikin abubuwan da suka faru a wannan makon har da abin jimami inda ruwa ya yi sanadiyar halaka wasu a jihar Kaduna.

Al'ummar yankin Rigasa dai sun fada cikin jimami da zulumi tun bayan batan mutum hudu ciki har da wata budurwa wadda kwanaki kalilan ya rage a daura mata aure.

Iftila'in ya faru ne ranar Litinin bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi awon gaba da abin hawan da suke tafiya a cikinsa.

Saurayin yarinyar, Mubarak Ibrahim Abubakar ya shaida wa BBC cewa tun ranar Litinin din ake nema amma Allah bai sa an dace ba, "don har kauyukan da ke makwabtaka da mu an kai cigiya amma shiru ba labari.